Nazir Dan Hajiya furodusa ne fitacce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood yayi fina finai da dama a masana'antar Yana furodusin Wakoki.[1]

Takaitaccen Tarihin sa gyara sashe

Nazir Dan hajiya an haife shi a ranar 4 ga watan Ogusta shekarar 1987 a Jihar Filato garin Jos. Yayi karatun firamare a garin Jos sannan yayi karatun sakandiri a jihar gombe . Daga Nan ya tafi Jihar Kano yayi karatun diploma har zuwa HND a fannin business administration and management a makarantar state polytechnic Kano.[2] Nazir Dan hajiya yayi aure da mata daya da Yara.[3]

Masana antar fim gyara sashe

Yadda ya shiga masana'antar fim shine, akwai Yar uwarsa jamila Nagudu sadda yake karatun difloma tace ya kamata ya Sami abinda ze dinga tallafa ma kansa a karatu. Ya fara da editing ne a Wani fim Mai suna"karshe furuci" fim din na Jamila ne a kamfanin jamnaz entertainment. Bayan ya gama karatun difloma ya fada harkan sosai.[4]

  • Fina Finan Sa
  • Mai farin jini
  • Karshe furuci
  • Alkuki
  • Gamdakatar
  • halwa
  • Maja

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.hausaloaded.com/tag/nazir-dan-hajiya
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
  3. http://arewakonnect.blogspot.com/2017/01/happy-married-life-to-nazir-dan-hajiya.html?m=1
  4. https://aminiya.ng/naziru-dan-hajiya-burina-kannywood-ta-zama-masanaantar-fim-ta-farko-a-duniya/