Yacouba Nasser Djiga (an haife shi a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2002) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Burkina Faso Kungiyar Kwallon Kafa wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya, a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Basel a gasar Swiss Super League, da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burkina Faso.[1]

Nasser Djiga
Rayuwa
Haihuwa Bobo-Dioulasso, 15 Nuwamba, 2002 (21 shekaru)
ƙasa Burkina Faso
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Tsayi 187 cm

Sana'a/Aiki

gyara sashe
 
Nasser Djiga a cikin kulub din su

Djinga ya buga wasan kwallon kafa ta matasa tare da Vitesse FC a Burkina Faso. Bayan da ya samu kiraye-kiraye daban-daban zuwa kungiyarsu ta farko kuma ya fara bugawa kungiyarsa wasa a wasannin karshe na kakar 2018-19, ya ci gaba zuwa kungiyarsu a kakar wasa ta 2019-20. Djinga ya buga masu wasanni 14, inda ya zura kwallo daya, a rukunin Deuxième mataki na biyu na kwallon kafa a Burkina Faso. Duk da lokacin da ya rage ba a kammala ba saboda cutar COVID-19, saboda ƙungiyar ta kasance shugabannin lig, sun sami nasarar ci gaba zuwa gasar Premier ta Burkinabé. A kakar wasa ta gaba Djinga ya kasance dan wasa kuma yawan wasa akai-akai a kungiyar. Ya samu kira zuwa tawagar Burkina Faso U-20 kuma ya buga musu wasanni hudu a gasar cin kofin Afrika na U-20 na 2021.[1][2][ana buƙatar hujja]

A lokacin kasuwar musayar 'yan wasa a lokacin bazara na 2021, Djiga ya rattaba hannu a kan babbar kungiyar FC Basel ta Switzerland bayan samun sha'awar garesa Lille OSC a gasar Ligue 1 ta Faransa da kungiyoyin Belgium da Spain. Basel sun sanar da sanya hannu a ranar 19 ga watan Yuni.[2]

Bayan buga wasanni biyar na gwaji, a ranar 29 ga Yulin 2021, Djinga ya yi karo da tawagar farko ta FC Basel a lokacin da ta doke Partizani da ci 2-0, a zagaye na biyu na cancantar shiga gasar cin kofin Europa na 2021–22. Abin takaici Djinga ya ji rauni a lokacin wasan kuma an tilasta masa fita na tsawon makwanni shida sakamakon raunin da ya samu a kafar hagu. Ya koma kungiyar ne a ranar 19 ga watan Satumba domin buga wasan cin kofin Swiss Cup da kungiyar armature FC Rorschach-Goldach.

A ranar 24 ga Oktoba Djiga ya buga wasansa na farko na Super League ga sabon kulob dinsa a wasan gida a St. Jakob-Park yayin da Basel ta ci Lugano 2-0 kuma ya buga wasan gaba daya.[3]

Ayyukan kasa

gyara sashe

Djiga ya fara fafatawa da 'yan wasan Burkina Faso a wasan sada zumunci da suka doke Kosovo da ci 5-0 a ranar 24 ga Maris, 2022.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Yacouba Nasser Djiga, la pépite qui fait craquer de grands clubs". burkina24.com.
  2. 2.0 2.1 FC Basel 1893 (19 June 2021). "Der FCB verpflichtet Yacouba Nasser Djiga". FCB signed Yacouba Nasser Djiga. FC Basel homepage. Retrieved 2021-06-19.
  3. FC Basel 1893 (24 October 2021). "Wieder ein Dreier–der FCB Schlägt Lugano 2:0". Another three pointer - FCB beat Lugano 2-0. FC Basel homepage. Retrieved 2021-10-24.
  4. Verein "Basler Fussballarchiv” (19 September 2021). "FC Rorschach-Goldach 17 - FC Basel 0:3 (0:1)". Verein "Basler Fussballarchiv”. Retrieved 2021-09-19.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe