Nana Klutse
Nana Ama Browne Klutse tana nazarin canjin yanayi na Afirka ta Yamma. Aikinta yana mai da hankali ne kan kimiyyar yanayi da ci gaba musamman kan Damuwar kasashen Afirka.[1][2] Ita ce babbar malama a Sashin ilimin kimiyyar lissafi, Jami'ar Ghana. A baya, tana kula da Cibiyar hangen nesa da yanayi. Dokta Klutse masanin Kimiyyar Yanayi ce ta cibiyar Nazarin Lissafi ta Afirka kuma babban marubuciya CE dake ba da gudummawa ga Rahoton Bincike na shida na IPCC (AR6). Ta kuma karfafa gwiwa ga 'yan mata a kasar Ghana don yin la'akari da ayyukan kimiyya da kuma tallafawa ci gaban ilimin kimiyya a kasar.
Nana Klutse | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 23 Mayu 1981 (43 shekaru) |
ƙasa | Ghana |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Cape Town (13 ga Faburairu, 2007 - 9 Disamba 2012) Doctor of Philosophy (en) |
Sana'a | |
Sana'a | climatologist (en) da researcher (en) |
Employers |
University of Cape Coast (1 Satumba 2004 - 1 ga Faburairu, 2011) University of Cape Coast (2 ga Faburairu, 2011 - 1 Oktoba 2011) Ghana Atomic Energy Commission (en) (1 Oktoba 2011 - 31 ga Yuli, 2018) University of Ghana (1 ga Augusta, 2018 - 31 ga Janairu, 2021) African Institute for Mathematical Sciences Rwanda (en) (1 ga Maris, 2020 - |
Mamba | International Astronomical Union (en) |
Kwarewar sana'a
gyara sasheDokta Klutse ta yi aiki a Cibiyar Kimiyyar Sararin Samaniya da Fasaha ta Ghana na Hukumar Kula da Makamashin Atom a matsayin babban masanin kimiyyar bincike daga shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2018. Kafin wannan, ta kasance bakon malama a Cibiyar Bayar da Ilimin Kimiyyar Yammacin Afirka kan Yanayi da Ingantaccen Amfani da Kasa (WASCAL) da ke Akure, Kasar Najeriya.[3][4][5][6]
Siyasa
gyara sasheDokta Klutse kuma tana aiki a cikin siyasa a matsayin memba na National Democratic Congress.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Klutse, NAB et al. (2016). Daily characteristics of West African summer monsoon precipitation in CORDEX simulations. Theoretical and Applied Climatology, 123(1-2): 369-86.
- ↑ Klutse NAB et al (2018). Potential impact of 1.5 °C and 2 °C global warming on consecutive dry and wet days over West Africa. Environmental Letters, 13(5). https://doi.org/10.1088/1748-9326/aab37b
- ↑ Donkor, Kwadwo Baffoe (26 July 2019). "Dr Nana Ama Browne Klutse joins NDC Abura Asebu Kwamankese race". Graphic Online. Retrieved 8 January 2021.
- ↑ "Nana Ama Browne Klutse: Ghanaian scientist studies dynamics of west African monsoon". Future Climate for Africa. 21 December 2016. Retrieved 8 January 2021.
- ↑ "AIMS announces first cohort of women in Climate Change Science Fellows". 2018-05-15.
- ↑ Ampofo, Obrempong (26 February 2018). "Mfantseman: Science teachers trained in effective teaching methods". Citi 97.3 FM News. Retrieved 3 April 2020.