Kwamfuta na’ura ce mai aiki da wutan lantarki, da ƙwaƙwalwa, wajen karɓa da sarrafawa da adanawa da kuma miƙa bayanai, a sigogi daban-daban. Wannan shine ta’arifin kwamfuta a takaice. Bayan haka kwamfuta na tattare ne da manyan ɓangarori guda biyu; ɓangaren gangan jiki, wanda aka fi sani da Hardware, a turance. Sai kuma ɓangaren ruhi ko rai, wanda ake kira Software (manhaja), shima a turance. Kafin mu yi nisa, mai karatu zai ji ana fassara kalmomin turancin nan, saɓanin yadda zai gamsu ko yake ganinsu a cikin ƙamus (Dictionary). Hakan kuma ya faru ne saboda a yanzu muna cikin wani zamani ne mai suna “turban masana”, ko Information Highway, kamar yadda bayani ya gabata a ƙasidar Matambayi ba ya ɓata. A wannan zamani, kalmomin harsunan duniya za su yi ta sauyawa ne iya gwargwadon fannin ilimi ko rayuwar da ake amfani da su. Don haka sai a kiyaye.[1]

Komfuta

Amfani da komfuta

gyara sashe
 
Na'ura.
 
Na'urar tafi da gidanka.
 
Na'ura.
 
 
 
CP NeXTstation.
 
 
Hoton komfuta kiran kamfanin Apple.

Kwamfutoci ana amfani dasu wurin aiwatar da kuma ayyuka a kamfani, masana'anta da kayayyakin da ake aiki a gidaje dasu. waɗannan kwamfutoci sun haɗa da ƙananan kayayyaki har da manyansu, kamar abin dafa abinci na Microwave, Rimotin tsara TV, Robotics, na'urar komfuta' wayar hannu da sauransu. Kwamfutocin da aka ƙirƙira da farko anyi sune dan taimaka wa mutane yin lissafi kawai, kamar 'abacus'. Sannan ansama cigaba a rayuwar Dan'adam, ta yadda yafara kirkiran sabbin kwamfutoci dazasu taimakesa wurin yin ayyuka masu wahala da daukan lokaci. Na'urar da aka fara ƙerawa na kwamfuta dake amfani da wutan lantarki sune waɗanda kuma aka ƙera su a lokacin ƴaƙin duniya na II. Kwamfutoci na zamani da ake yinsu ayanzu suna ɗauke da []injina]]n dake aiwatarwa da gudanar da ayyuka a cikinsu, kamar sashin gudanarwa da ake kira da turanci central processing unit (CPU), da kuma wani ɓangare na ƙwaƙwalwan kwamfutar dake kula da ajiye abubuwan da aka sanya aciki. Shi dai fannin gudanarwa ta kwamfuta itace ke aiwatar da ayyukan daya danganci lissafi da nazarce nazarce da sauransu.

Fannonin komfuta

gyara sashe
 
wani bangare na kwamfuta
 
daya daga cikin bangarorin komfuta kenan
 
bangaran kumfuta

Akwai Fannoni daban daban dasuka haɗa kwamfuta, akwai fannin kayayyakin dake waje wato output devices da na ciki wato input devices da kuma kayayyakin dake sanya aiki acikin kwamfutar da waɗanda ake saukar da aiki dasu daga cikin kwamfuta. Waɗannan sune; keyboards, mice, joystick, monitor screens, printers, touchscreen. kwamfuta nada matuƙar amfani a rayuwar ɗan Adam.

Manazarta

gyara sashe