Mustapha Muhammad Inuwa shine tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma tsohon Kwamishinan ilimi na jihar Katsina.

Mustapha Muhammad Inuwa
Rayuwa
Sana'a

Rayuwar farko

gyara sashe

An haife shi a ƙaramar hukumar Ɗan Musa a jihar Katsina.

Mustapha Muhammad Inuwa ya taɓa zama malami a Usman Ɗan Fodiyo daga shekarar 1984 - 1999,[1] sannan ya zama Kwamishinan ilimi a jihar Katsina daga shekarar 2003 - 2006, sakataren gwamnatin jihar Katsina na musamman daga 2006 - 2007.

Ya yi murabus daga muƙaminsa na SSG ga gwamnatin jihar Katsina domin ya tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Katsina[2] a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress[3] [4] kuma ya sha kaye a kan Umar Dikko Radda . [5] Ya yi alƙawarin marawa Umar Dikko Raɗɗa baya a wannan aiki nasa.[6]

An zarge shi a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ke taimakawa ayyukan garkuwa da mutane a jihar Katsina tun lokacin da Aminu Bello Masari ya kuma hau an mulki. Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya bayyana cewa ya gana da ‘yan bindigar a lokuta biyu ko fiye da haka, inda ya tattauna da su domin warware matsalar tada ƙayar baya a jihar, amma ya musanta goyon bayan ayyukan ‘yan fashin da suke yi a jihar,[7] yana mai cewa., "Ni ma an sha fama da hare-haren rashin tausayi nasu."[8] Yayin tattaunawa da manema labarai ya ƙara da cewa “Na yi amfani da babur na je na gana da shugabanninsu. Na ce musu zan zauna da su a sansaninsu, domin shugabansu ya je ya tattauna da mai martaba.

“Na ce musu idan shugabansu ya dawo su bar ni in je, idan kuma bai dawo ba, duk abin da aka yi masa su yi min. Na yi haka ne domin ina so kuma har yanzu ina son zaman lafiya. Na san Haɗarin da ke tattare da hakan amma na amince da gwamna kuma na san da gaske muke wajen yaƙar rashin tsaro.”[9]

Mustapha Inuwa ya taɓa gabatar da Musa a gaban wata kotu bisa zarginsa da taimakawa ‘yan fashi a jihar Katsina.[10]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.katsinastate.gov.ng/governorsoffice/principal-officers/
  2. https://independent.ng/inuwa-katsina-sgs-formally-tenders-his-resignation-letter/
  3. https://punchng.com/2023-supporters-endorse-katsina-ssgs-gov-ambition/
  4. https://hausa.legit.ng/siyasa/1466974-katsina-sakataren-gwamnati-mustapha-inuwa-ya-yi-murabus-daga-kan-mukaminsa/
  5. https://dailypost.ng/2022/04/22/2023-guber-katsina-ssg-resigns/
  6. https://www.channelstv.com/2022/05/28/katsina-apc-guber-primary-inuwa-concedes-defeat-pledges-to-support-dikko-radda/
  7. https://dailytrust.com/those-linking-me-to-katsina-killings-mischievous-ssg
  8. https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/517789-katsina-ssg-speaks-on-his-relationship-with-bandits.html
  9. https://reportdailys.com/tag/dr-mustapha-muhammad-inuwa/
  10. https://21stcenturychronicle.com/katsina-ssg-drags-man-to-court-for-linking-him-with-banditry/