Mumannaʿa bint ʿAmr (Larabci: ممنعة بنت عمرو‎) ta kasance matar Abd al-Muttalib ce.

Mumanna'a bint Amr
Rayuwa
ƙasa Makkah
Ƴan uwa
Abokiyar zama Abdul-Muttalib
Yara
Sana'a

Ta fito ne daga kabilar Khuza'a a Makka. Mahaifinta shi ne Amr ibn Malik ibn Mu'ammal ibn Suwayd ibn As'ad ibn Mashnu ibn Abd ibn Habtar ibn Adi ibn Salul ibn Ka'b ibn Amr. [1]:100

Mijinta na farko shi ne Abd Awf ibn Abd, daga dangin Zuhra na Quraysh. Ɗansu, Awf, shi ne mahaifin Abd al-Rahman ibn Awf. [1]:101

Daga baya ta auri Abd al-Muttalib. Ɗanta daga wannan auren shine Mus'ab ibn Abd al-Muttalib, wanda aka fi sani da al-Ghaydaq saboda karamcinsa.[1] Kodayake, Ibn Hisham bai ambaci Mus'ab ba. Ya tabbatar da cewa Hajl ibn Abd al-Muttalib, ɗan Abd al-muttalib da Hala bint Wuhayb, shine wanda aka sani da al-Ghaydaq.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 Muhammad ibn Saad. Kitab al-Tabaqat al-Kabir. Translated by Haq, S. M. (1967). Ibn Sa'd's Kitab al-Tabaqat al-Kabir Volume I Parts I & II. Delhi: Kitab Bhavan.
  2. Abdulmalik ibn Hisham. Notes to Ibn Ishaq's Sirat Rasul Allah. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad, p. 707 note 97. Oxford: Oxford University Press.