Muhammad Hanif Malik

Dan siyasa ne a Pakistan

Muhammad Hanif Malik Awan ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya taɓa zama memba na Majalisar Lardin Punjab, daga shekarar 1997 zuwa ta 1999 da kuma daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018. Ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan daga watan Disambar 2012 zuwa watan Maris na shekarar 2013.

Muhammad Hanif Malik
Rayuwa
Haihuwa Gujrat (en) Fassara, 5 Mayu 1952 (71 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Pakistan Muslim League (N) (en) Fassara

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haife shi a ranar 5 ga watan Mayun 1952 a Gujrat .[1]

Ya sami ilimin matakin digiri .[1]

Harkokin siyasa gyara sashe

Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PP-95 (Gujrat-cum-Jhelum) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1993 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 20,726 sannan kuma ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-J).[2]

An zaɓe shi a Majalisar Lardi ta Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (PML-N) daga Mazaɓar PP-95 (Gujrat-cum-Jhelum) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1997 . Ya samu ƙuri'u 29,854 sannan ya doke ɗan takarar PML-J.[2]

Ba zai iya tsayawa takara a babban zaɓen shekarar 2002 ba saboda buƙatar kammala karatun digiri.[3]

An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan daga Mazaɓar NA-107 (Gujrat-IV) a matsayin ɗan takarar PML-N a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a shekarar 2012.[3][4] Ya samu ƙuri'u 70,434 sannan ya doke Rehman Naseer ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-Q).[5]

An sake zaɓen shi a Majalisar Lardi ta Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-114 (Gujrat-VII) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013 .[6] Ya samu ƙuri'u 40,428 sannan ya doke Raja Muhammad Naeem Nawaz ɗan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).[7]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Punjab Assembly". www.pap.gov.pk. Retrieved 21 January 2018.
  2. 2.0 2.1 "Punjab Assembly election result 1988-97" (PDF). ECP. Archived (PDF) from the original on 30 August 2017. Retrieved 26 March 2018.
  3. 3.0 3.1 Azeem, Muhammad (18 March 2013). "Man having links with banned outfit may get PML-N ticket". DAWN.COM. Retrieved 21 January 2018.
  4. Butt, Waseem Ashraf (26 April 2013). "'N' suffers a double blow in Gujrat". DAWN.COM (in Turanci). Retrieved 26 July 2017.
  5. "By-elections: PML-N shows strength in Punjab, bags 7 of 8 seats - The Express Tribune". The Express Tribune. 5 December 2012. Retrieved 25 May 2018.
  6. "List of winners of Punjab Assembly seats". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 21 January 2018.
  7. "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 25 May 2018.