Moussoro

Wuri ko yanki a cikin Barh El Gazel, Chadi

Moussoro ( Larabci: موسورو‎ ) wani gari ne a kasar Chadi, yana a dai-dai nisan kilomita 300 (mil 190) daga arewa maso gabashin N'Djamena akan hanyar Faya-Largeau. Wata muhimmiyar cibiyar sufuri, tana a wurin Kogin Bed kuma a sakamakon haka akwai ciyayi da yawa a yankin.[ana buƙatar hujja]

Moussoro


Wuri
Map
 13°38′N 16°29′E / 13.63°N 16.48°E / 13.63; 16.48
Ƴantacciyar ƙasaCadi
Region of Chad (en) FassaraBahr el Gazel
Department of Chad (en) FassaraBarh El Gazel Sud (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 16,349 (2009)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 304 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Moussoro babban birni ne na yankin Barh El Gazel (Bahr el Gazel).[1] Filin jirgin sama na Moussoro ne ke hidima a garin ga masu zirga-zirga ta sama. Moussoro na cikin ƙabilar Gouran (Krreda) (Karra) na arewacin Chadi. Ya zama garin kasuwancin da gudanarwar jama'ar. Ranar kasuwar Moussoro ita ce ranar Alhamis. Yawanci an san su da aikin noma.[ana buƙatar hujja]

Akwai gidan shugaban ƙasa na biyu a Moussoro, bayan na farkon kuma babban da ke a birnin N'djamena ( duba hoton da ke ƙasa ). Garin kuma shi ne babban yankin da ake horar da sojoji a kasar Chadi.[ana buƙatar hujja]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Profil National du Tchad sur la gestion des produits chimiques, Troisieme Edition" [National Profile of Chad on Chemicals Management, Third Edition]. ESTIS.net (in French). Republique du Tchad - Ministere de l'Environnement et des Ressources Halieutiques [Republic of Chad - Ministry of Environment and Water Resources]. September 2009. Archived from the original (PDF) on 1 March 2014.CS1 maint: unrecognized language (link)