Mojisolaoluwa Alli Macaulay
MojisolaOluwa Kehinde Alli – Macaulay (née Alli) (an haife ta a ranar 10 ga watan Oktoban, 1977[1]) 'yar siyasan Najeriya ce,[2] 'yar majalisa[3][4][5][6] kuma 'yar jam’iyyar All Progressive Congress APC. Ta kasance 'yar majalisar dokokin jihar Legas, mai wakiltar mazabar Amuwo Odofin I[7] kuma shugabar kwamitin majalisar dokokin jihar Legas mai kula da harkokin mata, rage talauci da samar da ayyukan yi.[8]
Mojisolaoluwa Alli Macaulay | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Surulere, 10 Oktoba 1977 (47 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Milton Keynes (en) 2003) diploma (en) Jami'ar Jihar Lagos Bachelor of Arts (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Kuruciya
gyara sasheAn haifi Mojisolaoluwa a garin Surulere, jihar Legas kuma ta fito daga tsibirin Legas-Island da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Ilimi
gyara sasheTa yi karatun ta na firamare a Subola Nursery & Primary School 1982-1984 kuma ta kammala a Festac Primary School 1984-1990. Nan da nan ta fara karatun sakandare a makarantar sakandare ta 'yan mata ta Festac 1990-1993[9][10] kuma ta kammala a Makarantar Sakandare ta Navy Town a tsakanin shekarun 1993-1995[11] inda ta sami takardar shaidar Makarantun Yammacin Afirka (WAEC).
Ta ci gaba da karatun ta na Diploma a Open University Milton Keynes, United Kingdom[12][13] a cikin ilimin zamantakewa (2003).[11] A shekarar 2015 ta kammala Digiri dinta na farko a fannin tarihi da huldar kasa da kasa[14] daga Jami’ar Jihar Legas.[1] A 2021 kuma ta sami digiri a LAW a Jami'ar Jihar Lagos.
Rayuwa ta sirri
gyara sasheTa auri Honourable Jonathan Macaulay kuma suna da yara biyu.[15]
Aiki
gyara sasheMojisolaoluwa ta fara aikinta akan jarida da yada labarai a shekarar 1997 a matsayin mai bayar da sanarwar Duty na Rediyon Lagos/Eko FM (1997-1999) [1], nan take ta yi aiki a matsayin mai gabatar da labarai a MITV/STAR FM na tsawon shekaru uku. 1999-2001), sannan ta koma NTA 2 Channel 5 a matsayin Mai Binciken Labarai, Mai gabatar da Labarai sannan kuma mai gabatarwa (2001-2002).
Aikin siyasa
gyara sasheTa tsaya takarar kansila a WARD B1, Amuwo Odofin a karkashin jam'iyyar Action Congress of Nigeria kuma ta yi nasara a shekarun (2010 -2013) [2] . Ta kuma kasance tsohuwar mataimakiyar shugaba, Amuwo Odofin na majalisar dokoki, karamar hukumar Amuwo Odofin.[16]
A cikin shekara ta 2019 ta fito takarar kuma ta yi Nasarar zaman 'yar majalisa a Mazabar Amuwo Odofin 1. A halin yanzu ita mamba ce a majalisar dokoki ta 9, majalisar dokokin jihar Legas.[17]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Who be Mojisola Alli-Macaulay? wey say "Nigerian youths dey high on drugs all di time"". BBC News Pidgin. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "MOJISOLA ALLI-MACAULAY: Newbies in politics should not aim for high positions". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. March 1, 2020. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly" (in Turanci). Archived from the original on May 12, 2021. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "My drug comment about hoodlums, not youths — Lagos lawmaker". Punch Newspapers (in Turanci). April 16, 2021. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "EMPOWERMENT: Lagos lawmaker urges youths to support govt". Vanguard News (in Turanci). April 10, 2021. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly" (in Turanci). Archived from the original on May 12, 2021. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "Constituencies – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "Admin. "More space for women equals a better Africa – Hon. Mojisolaoluwa Alli-Macaulay | National Daily Newspaper". Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "'Amuwo Odofin constituency 'll benefit from my stewardship'". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. February 24, 2019. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
- ↑ 11.0 11.1 "Who be Mojisola Alli-Macaulay? wey say "Nigerian youths dey high on drugs all di time"". BBC News Pidgin. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "Who be Mojisola Alli-Macaulay? wey say "Nigerian youths dey high on drugs all di time"". BBC News Pidgin. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
- ↑ 'Amuwo Odofin constituency 'll benefit from my stewardship'". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. February 24, 2019. Retrieved May 12, 2021.
- ↑ "Members – Lagos State House of Assembly". Retrieved July 12, 2021.