Milly Nassolo
Milly Nassolo Kikomeko 'yar kasuwan zamantakewar jama'a ce ta Uganda, mai fafutuka kare hakkin ɗan Adam kuma lauya. Ita ce ta kafa gidauniyar Maisha Holistic Africa, wata kungiya mai zaman kanta da ke gundumar Kagadi. [1] [2] [3] [4]
Milly Nassolo | |||||
---|---|---|---|---|---|
2013 -
2013 - | |||||
Rayuwa | |||||
ƙasa | Uganda | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Mpigi Mixed Secondary School (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | social entrepreneur (en) , Lauya da Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Nassolo a ƙauyen Kikumbo, ƙaramar hukumar Kibibi, a gundumar Butambala. Ta halarci makarantar firamare ta Gombe, sannan ta yi karatun firamare, sai kuma Mpigi Mixed Secondary School for O-Level, sannan ta yi karatun A-level a makarantar sakandaren Mpigi. Ta sami digiri na farko a fannin shari'a a Kampala International University. [4]
Sana'a
gyara sasheTun daga shekarar 2014, Nassolo tana aiki a matsayin mataimakiyar lauya a Lubega, Ssaka da Co. Advocates yayin da take karatun digiri. [4] [5] [6] A cikin shekarar 2014, ta kafa Maisha Holistic Africa Foundation, [7] [2] kungiya mai zaman kanta a gundumar Kagadi [8] [9] [10] amma an kaddamar da kungiyar a shekarar 2019. [11] [12]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheNassolo ta auri Robert Kikomeko Tumusabe a cikin shekara ta 2016 a Kamwokya Church of God. Tare, suna da 'ya'ya maza biyu, Tyler Kaeb K. Tumusabe da Travis Silver K. Tumusabe [2] [13] [14]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Editorial, PML DAILY EDITOR | PML Daily (October 26, 2023). "MILLY NASSOLO: Passion for Empowering Women".
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Asingwire, Mzee (May 17, 2023). "Milly Nassolo's legal career: Balancing law practice and activism for social change". Pulse Uganda. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "auto1" defined multiple times with different content - ↑ "Milly Nassolo Unveils Maisha Holistic Africa Foundation in Kagadi District | the Kampala Post".
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "Working for women makes Nassolo happy". Monitor. March 28, 2021. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "auto" defined multiple times with different content - ↑ "Activist Milly Kikomeko Launches "Get Talking with Milly" Tweet Chat Initiative – TowerPostNews". thetowerpost.com. October 26, 2023.
- ↑ Wampula, Arajab (October 25, 2023). "Here Are All The Amazing Things Milly Nassolo Is Doing To Advocate For The Girl Child* | DaParrot | Building Communities, Outlining Possibilities".
- ↑ "Nassolo supports disadvantaged people". Bukedde.
- ↑ Adeya, John Kenny (October 19, 2023). "Milly Nassolo Fostering Children's and Women's Rights in Uganda". Kampala Edge Times.
- ↑ Mugisha, Mugibson (May 18, 2023). "Meet Milly Nassolo: A Champion For A Brighter Future For Children & Women In Uganda - MUGIBSON". mugibson.com.
- ↑ Mugisha, Mugibson (February 1, 2023). "Activist Milly Nassolo Extends Helping Hand Through Health Camp In Kagadi District - MUGIBSON". mugibson.com.
- ↑ "Through Maisha Holistic Africa Foundation, Social Entrepreneur Milly Nassolo Seeks to Help Those in Need - MUGIBSON". 17 April 2019.
- ↑ "Social Entrepreneur Milly Nassolo Launches Maisha Holistic Africa Foundation". 17 April 2019.
- ↑ Lisimba, Hillary (December 21, 2021). "I lied to him about everything the first time we met, Ugandan wife discloses". Tuko.co.ke - Kenya news.
- ↑ "Social Entrepreneur Milly Nassolo Launches Maisha Holistic Africa Foundation". 17 April 2019.