Mathilde-Amivi Petitjean
Mathilde-Amivi Petitjean (An haife ta a watan Fabrairu 19, 1994 [1] [2] ) 'yar wasan gudun kankara ce ta zagayen ƙasa 'yar ƙasar Faransa da Togo. Ta yi wa kasar Togo wasa a gasar Olympics na lokacin sanyi a shekara ta 2014 a tseren gargajiya na kilomita 10.[3] Petitjean ta kare a matsayi na 68 a tserenta guda daya tilo da ta yi a tsakanin 'yan wasa 75, kusan mintuna goma a bayan wacce tazo na daya wato Justyna Kowalczyk ta Poland. Petitjean na fatan cewa bayyanarta zai taimaka wajen zaburar da matasan Afirka don shiga cikin wasanni na hunturu.[4]
Mathilde-Amivi Petitjean | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kpalimé, 19 ga Faburairu, 1994 (30 shekaru) |
ƙasa | Togo |
Karatu | |
Makaranta |
Savoy Mont Blanc University (en) Emlyon Business School (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | sportsperson (en) da cross-country skier (en) |
Mahalarcin
| |
Nauyi | 60 kg |
Tsayi | 163 cm |
An haifi Petitjean a Togo, ga mahaifiya 'yar Togo wanda hakan ya ba ta damar yi wa kasar wasa. Kungiyar Ski ta Togo ta tuntube ta a cikin watan Maris 2013 ta kafar Facebook don yi wa kasar wasa a gasar Olympics na lokacin sanyi. Petitjean ta kwashe mafi yawan rayuwarta a Haute-Savoie, Faransa, inda ta koyi wasan tsaren kankara.[5]
Ta dauki tutar Togo a wajen bikin bude taron.[6]
Ta yi wa kasar Faransa wasa har zuwa lokacin da ta canza sheka zuwa Togo.
Cross-country skiing results
gyara sasheAn samo duk sakamakon daga Ƙungiyar Ski ta Duniya (FIS).
Wasannin Olympics
gyara sasheShekara | Shekaru | 10 km </br> mutum guda |
15 km </br> skiathlon |
30 km </br> taro fara |
Gudu | 4 × 5 km </br> gudun ba da sanda |
Tawaga </br> gudu |
---|---|---|---|---|---|---|---|
2014 | 20 | 66 | - | - | - | - | - |
2018 | 24 | 83 | - | - | 59 | - | - |
Gasar Cin Kofin Duniya
gyara sasheShekara | Shekaru | 10 km </br> mutum guda |
15 km </br> skiathlon |
30 km </br> taro fara |
Gudu | 4 × 5 km </br> gudun ba da sanda |
Tawaga </br> gudu |
---|---|---|---|---|---|---|---|
2017 | 23 | - | - | - | 49 | - | - |
Gasar cin kofin duniya
gyara sasheMatsayin yanayi
gyara sasheKaka | Shekaru | Matsayin ladabtarwa | Matsayin yawon shakatawa na Ski | |||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Gabaɗaya | Nisa | Gudu | Nordic </br> Budewa |
Yawon shakatawa de </br> Ski |
Gasar cin kofin duniya </br> Karshe |
Yawon shakatawa na Ski </br> Kanada | ||
2016 | 22 | NC | NC | NC | - | - | N/A | DNF |
2017 | 23 | NC | - | NC | - | - | DNF | N/A |
2018 | 24 | NC | NC | NC | - | - | - | N/A |
Manazarta
gyara sashe- ↑ Mumuni, Moutakilou (16 January 2014). "Togo: Sochi Olympics 2014 – Mathilde Petitjean Amivi Proud to Represent Togo" . AllAfrica.com . Retrieved 18 January 2014.
- ↑ "PETITJEAN Mathilde-Amivi" . FIS-Ski . International Ski Federation. Retrieved 5 January 2020.Empty citation (help)
- ↑ Laura (29 January 2014). "Le Togo allongera la liste des pays tropicaux aux jeux d'hiver" . www.french.china.org.cn (in French). Retrieved 29 January 2014.
- ↑ Willemsen, Eric (13 February 2014). "Togo's 1st Winter Olympian Wants to Inspire Africa" . Associated Press . Krasnaya Polyana , Russia : ABC News . Retrieved 13 February 2014.
- ↑ Spillane, Chris; Woussou, Kossi (7 February 2014). "Mathilde-Amivi Petitjean skis cross-country from France to Sochi via Togo" . Sydney Morning Herald. Johannesburg , South Africa . Retrieved 8 February 2014.
- ↑ "Sochi 2014 Opening Ceremony – Flagbearers" (PDF). olympic.org . Sochi 2014 Olympic and Paralympic Organizing Committee . 7 February 2014. Retrieved 7 February 2014.