Masarautar Gaya
Masarautar Gaya ɗaya ce daga cikin sabbin masarautu huɗu da aka ƙirƙiro a jihar Kano a Najeriya. Gwamnatin jihar Kano ce ta kafa ta a shekarar 2019 kuma tana cikin ƙaramar hukumar Gaya.[1][2]
Masarautar Gaya | ||||
---|---|---|---|---|
Isamic Government (en) | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 2019 | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Babban birni | Gaya | |||
Dissolved, abolished or demolished date (en) | 23 Mayu 2024 | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano |
Masarautar Gaya tana ƙarƙashin jagorancin wani basarake ne da aka fi sani da Sarkin Gaya, wanda gwamnatin jihar Kano ta naɗa. Sarkin Gaya na yanzu shine Aliyu Ibrahim, wanda aka naɗa a shekarar 2021 bayan rasuwar marigayi sarki Alhaji Ibrahim Abdulkadir. Masarautar galibin al’umma ce ta noma, inda ake noman amfanin gona irin su shinkafa, masara, gero da gyaɗa da yawa.[3][4]
Al'adu
gyara sasheTa fuskar al’adu, da al’adun al’ummar Gaya suna da kyawawan abubuwan tarihi da suka shahara wajen bukukuwa masu kayatarwa irin su Durbur na Hawan Sallah da raye-rayen gargajiya. Daya daga cikin manyan bukukuwan da ake gudanarwa a Masarautar dai shi ne bikin Gada da ake yi a duk shekara, wanda kuma ya hada da baje kolin kokawa na gargajiya, da harbin bindiga, da sauran ayyukan al'adu.[5][6]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ Giginyu, Ibrahim Musa (2022-01-29). "The making of Gaya's third first-class emir". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-05-11.
- ↑ Ibrahim, Salim Umar (2022-01-29). "Dignitaries throng Gaya emirate as emir receives staff of office". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-05-11.
- ↑ "Ganduje announces Ibrahim Aliyu as new emir of Gaya". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2021-09-26. Archived from the original on 2023-05-11. Retrieved 2023-05-11.
- ↑ "Ganduje appoints Aliyu Ibrahim as new Emir of Gaya". TheCable (in Turanci). 2021-09-26. Retrieved 2023-05-11.
- ↑ "Kano's Sallah durbars after split emirates". Daily Trust (in Turanci). 2019-06-08. Retrieved 2023-05-11.
- ↑ Reporter, Our (2021-05-12). "Kano, Bichi, Gaya, Karate And Rank Emirates To Hold Hawan Sallah Tomorrow". Daybreak, Politics, Entertainment, Sport (in Turanci). Retrieved 2023-05-11.