Masallacin Maluwe
Masallacin Maluwe masallaci ne da ke kan titin Bole a gundumar Gonja ta Yamma a yankin Savannah na Ghana. Ya kasance a hukumance a yankin Arewa. Maluwe ƙaramin ƙauye ne gabas da Filin shakatawa na Bui.[1]
Masallacin Maluwe | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana |
Yankuna na Ghana | Yankin Savannah |
Gundumomin Ghana | West Gonja Municipal District |
Coordinates | 8°40′10″N 2°17′29″W / 8.66942°N 2.2915°W |
|
Tarihi
gyara sasheA cewar wani limamin masallacin, wani dan mishan ne daga kasar Mali ya gina shi. Ya gina masallatan laka guda biyar yayin da ya ratsa yankin a hanya.[2]
Siffofin
gyara sasheMasallacin yana da manyan katanga fiye da masallacin Larabanga. An gina masallacin da laka da salon Sudan kuma yana da hasumiyoyi guda biyu wadanda su ma sun fi masallacin Bole tsayi amma ba ya kai tsayin masallacin Banda Nkwanta.[3] Hakanan yana da buttresses biyu a gefen yamma wanda ya yi kauri da boxy.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Adventure Archives". Visit Ghana (in Turanci). Archived from the original on 2021-08-03. Retrieved 2020-08-15.
- ↑ "Ghana's Historic Mosques: Maluwe". The Hauns in Africa (in Turanci). 2018-05-26. Retrieved 2020-08-15.
- ↑ Lewis, Andrea. "Mosque in Maluwe". International Mission Board. Retrieved 2020-08-15.