Masallacin Badshahi (harshen Punjabiبادشاہی مسجد), masallaci ne a birnin Lahore, babban birnin kasar Pakistan Wanda aka gina shi a zamanin daular Mughal.[1] Masallacin dai an gina shi ne a yammacin birnin Lahore saitin karkatar tsohuwar ganuwar birnin na Lahore,[2] kuma ana ganin masallacin a matsayin wata babbar alama ta birnin.[3]

Masallacin Badshahi
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaPakistan
Province of Pakistan (en) FassaraPunjab (en) Fassara
Division of Pakistan (en) FassaraLahore Division (en) Fassara
District of Pakistan (en) FassaraLahore District (en) Fassara
BirniLahore
Coordinates 31°35′17″N 74°18′34″E / 31.5881°N 74.3094°E / 31.5881; 74.3094
Map
History and use
Opening1671
Shugaba Aurangzeb (en) Fassara
Addini Mabiya Sunnah
Maximum capacity (en) Fassara 100,000
Karatun Gine-gine
Material(s) sandstone (en) Fassara
Style (en) Fassara Mughal architecture (en) Fassara
Heritage
Parts Hasumiya: 8

Gwarzo Jarumi Aurangzeb ne ya gina Masallacin a shekara ta 1671, wanda ya dauki shekaru biyu kafin kammala gina shi, sai a shekarar 1673 aka kamala. Masallacin wata babbar muhimmiyar alama ce dake nuna salo irin name gine-ginen zamanin Mughal. Shine ya rage daga cikin manyan masallatan da daular Mughal ta gina a kasar Pakistan.[4] Bayan rushewar daular Mughal, Masallacin ya koma karkashin ikon daular Sikh da kuma daular mulkin mallaka ta Birtaniya, Wanda a yanzu Masallacin ya zama wata babbar alama ta kasar Pakistan.

Mazaunin sa gyara sashe

 
Masallacin Badshahi a Hazuri Bagh daga Lahore.
 
Daga cikin Masallacin Badshahi.

Massllacin na zaune ne a birnin Lahore, Pakistan.

Mashiga ko Babbar kofar Masallacin na daga gefen yammacin Hazuri Bagh, yana fuskantar sananniyar kofar Alamgiri ta Lahore, wadda take daga gabashin Hazuri Bagh. Sannan kuma dai Masallacin na a gaba da kofar Roshnai, daya daga cikin kofofin ganuwar birnin Lahore, wadda take daga gefen kudancin Hazuri Bagh

[5]

osque.[6]

Hotuna gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "Lahore's iconic mosque stood witness to two historic moments where tolerance gave way to brutality".
  2. "Badshahi Mosque". Ualberta.ca. Archived from the original on 3 December 2014. Retrieved 2 January 2014.
  3. "Holiday tourism: Hundreds throng Lahore Fort, Badshahi Masjid - The Express Tribune" (in Turanci). 9 October 2014. Retrieved 10 September 2016.
  4. Meri, Joseph (31 October 2005). Medieval Islamic Civilization: An Encyclopedia. Routledge. p. 91.
  5. Waheed ud Din, p.14
  6. IH Malik Sikandar Hayat Khan: A Biography Islamabad: NIHCR, 1984. p 127