Mansurah Isah tsohuwar ‘yar fim din Kannywood ce kuma darakta ce da aka haifa a ranar 25 ga Fabrairun.[yaushe?] Tana da kanwa mai suna Maryam Isah, wacce ita ma shahararriyar ’yar fim din Kannywood ce.

Farkon rayuwa da karatu

gyara sashe

Mansura Isah hazika ce wacce ta fara aiki a matsayinta na shugabar bidiyo ta mata ta farko a Kannywood kafin ta tsunduma cikin wasan kwaikwayo a karshen shekarun 1990. Mansura ta bar wasan kwaikwayo don ta zauna tare da mijinta, Sani Danja wanda shi ma shahararren dan wasan kwaikwayo ne. Sun yi aure a shekara ta 2007 kuma aurensu ya sami 'ya'ya huɗu, Khadijatul Iman, Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf.

Malama Mansura Isa tsohuwar ‘yar fim kuma mai tallafawa mata domin su zamo masu dogaro da kai a yanzu, ta hanyar koya musu kananan sana’o’in dogaro da kai a yankunan karkara da ma wasu sassan burane.

Fina-finai

gyara sashe

Mansura ta auri fitaccen dan`wasan kannywood wanda aka sani da Sani Musa Danja

Manazarta

gyara sashe