Mano Dayak
Mano Dayak (1949 - Disamba 15, 1995) sanannen mai fafutukar 'yancin Abzinawa ne, shugaba, mai fafutuka, masani kuma mai sasantawa. Ya jagoranci tawayen Abzinawa a yankin Ténéré, arewacin Nijar a shekarun 1990s. An haife shi a kwarin Tiden a cikin tsaunin Aïr (kusa da birnin Agadez ) a shekarar 1949. Ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama a shekarar 1995, wanda ya haifar da hasashen cewa bai yi hatsari ba.[1]
Mano Dayak | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Nijar |
Suna | Mano |
Sunan dangi | Dayak (mul) |
Shekarun haihuwa | 1950 da 1949 |
Wurin haihuwa | Tidène (en) |
Lokacin mutuwa | 15 Disamba 1995 |
Wurin mutuwa | Tsaunukan Air |
Sanadiyar mutuwa | accidental death (en) |
Dalilin mutuwa | aviation accident (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | rebel (en) , business executive (en) da tour guide (en) |
Muƙamin da ya riƙe | chief manager (en) da deputy chairperson (en) |
Ilimi a | Indiana University (en) |
A farkon rayuwarsa ya tafi Jami'ar Indiana da ke Bloomington, Indiana don yin karatun digiri na farko a fannin ilimin tatsuniyoyi, sannan ya yi digiri a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Sorbonne. A nan ƙasar Faransa ne ya haɗu da matarsa Odile, ɗaliba ce a fannin sanin halayyar ɗan adam wadda ta shirya kafa sana’ar yawon buɗe ido da shi a farkon shekarun 1970s.[1]
Nasara da gado
gyara sasheBayan jagorancin tawayen Abzinawa (wanda ya jagoranta daga tushe a Adrar de Bouss ), Mano Dayak ya sanya sunansa a matsayin marubucin litattafai masu muhimmanci da yawa kan al'adun Abzinawa da siyasa. Ya kuma yi aiki a matsayin jagorar Thierry Sabine yayin gangamin Paris–Dakar. Ƙungiyar Tuareg Tinariwen ta sadaukar da waƙa gare shi a cikin albam ɗinsu mai suna "Aman Iman". An sanya masa sunan filin jirgin saman Mano Dayak da ke Agadez.[ana buƙatar hujja]