Richard Mani Ougadja (an haife shi ranar 31 ga watan Janairu 1988) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Togo wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na kulob ɗin ASC Kara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo.

Mani Ougadja
Rayuwa
Haihuwa Togo, 31 ga Janairu, 1988 (36 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Ougadja ya fara buga wasa tare da tawagar kasar Togo a wasan sada zumunci da suka doke Guinea da ci 2-0 a ranar 5 ga watan Yuni 2021.[1]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Mani yayi aiki a matsayin malami na ilimin motsa jiki, kafin ya mai da hankali kan wasan kwallon kafa. Yana da shekaru 33 a lokacin da aka fara kiransa na farko a duniya. Shi ɗan'uwan ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne Mani Sapol. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. Strack-Zimmermann, Benjamin. "Togo vs. Guinea (2:0)" . www.national-football-teams.com .
  2. Infos, Togo (June 11, 2021). "Ougadja Mani : l'épervier à suivre de près" .

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe