Makarantar Unguwar Zoma ta Jihar Jigawa

Makarantar unguwar zoma ta jihar Jigawa itace makarantar farko ta unguwar zoma a jihar Jigawa dake arewacin Najeriya.

Makarantar Unguwar Zoma ta Jihar Jigawa
Bayanai
Iri makaranta
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 2010
nairaland.com…

Tarihi gyara sashe

 
Aisha Moh'd Kazaure

An ƙirƙiro makarantar ne a watan Maris na 2010 kuma Aisha Moh'd Kazaure, wacce ungozoma ce kuma malama ta kafa, saboda karancin ungozomomi a jihar ta Jigawa. Tallafin ya fito ne daga Sashin Bunƙasa Kasashen rainon Burtaniya wanda ya amince da cewa, yayin da akwai mutane miliyan biyar da ke zaune a jihar, akwai ungozomomi kasa da 30. [1]

Shigarwa gyara sashe

Ƴan mata za su iya shiga karatun idan suna da Takardun Ingilishi da Kimiyya. Waɗannan ƙananan ƙwarewa ne kamar yadda jahilcin mata ya wuce 90% a yankin. Dalibai yawanci mata ne kuma shekarunsu basu wuce ashirin [1] duk da cewa kashi 80% na ma’aikatan lafiya maza ne.

Sauran makarantu gyara sashe

A shekarar 2015, Jihar Jigawa ta ce tana da niyyar kafa wata Makarantar ungozoma a Hadejia.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Called to be a midwife in northern Nigeria, UK Government, Retrieved 2 February 2016
  2. Jigawa to establish Nursing School, 29 July 2016, NGRGuardianNews, Retrieved 2 February 2016