Majalisar dokokin Oyo ita ce bangaren kafa dokoki da gyaran dokoki da ƙirƙirar su na gwamnatin jihar Oyo ta Najeriya. Majalisar dokoki ce mai mambobi tare da mambobi talatin da uku 33 da aka zaba daga kananan hukumomi talatin da uku 33 na jihar.

Majalisar dokokin jihar Oyo
unicameral legislature (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jahar Oyo
Wuri
Map
 7°24′32″N 3°54′31″E / 7.40887027°N 3.90850833°E / 7.40887027; 3.90850833
taswirar Oyo a nigeria

Ayyukan yau da kullun na Majalisar sune ƙirƙirar sabbin dokoki, gyara ko soke dokokin da ke akwai da kuma kula da zartarwa. Ana zaben membobin majalisar na tsawon shekaru hudu tare da 'yan majalisar tarayya (majalisar dattijai da ta wakilai) da gwamnan jihar. Majalisar jihar tana yin taro sau uku a mako (Talata, Laraba da Alhamis) a harabar majalisar a cikin babban birnin jihar, Ibadan.

Shugaban majalisar a yanzu shi ne Adebo Ogundoyin .