Majalisar Dokokin Jihar Adamawa

Majalisar dokoki ta jihar Adamawa ita ce bangaren kafa dokokin gwamnatin jihar Adamawa. [1][2] Majalisar dokoki ce mai mambobi guda 25 da aka zaba daga kananan hukumomi guda 21 (Mazabar Jihohi). An kayyade kananan hukumomin da ke da yawan mabukata a mazabu biyu don ba da wakilci dai-dai. Wannan ya sanya adadin 'yan majalisa a majalisar dokokin jihar ta Adamawa guda 25.

Majalisar Dokokin Jihar Adamawa
unicameral legislature (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jihar Adamawa

Ayyukan yau da kullun na Majalisar sune ƙirƙirar sabbin dokoki, gyara ko soke dokokin da ke akwai da kuma kula da zartarwa. [3][4] An zabi membobin majalisar na tsawon shekaru hudu tare da 'yan majalisar tarayya (majalisar dattijai da ta wakilai). Majalisar jihar tana yin taro sau uku a mako (Talata, Laraba da Alhamis) a cikin majalisar a cikin babban birnin jihar, Yola.

Kakakin majalisar dokokin jihar ta Adamawa na 7 shine Iya Abbas. Jam'iyyar Democratic Party (PDP) itace jam'iyya mafi rinjaye da mambobi guda 13 yayin da All Progressive Congress ke da kujeru gyda 11 African Democratic Congress tana da guda 1 yana saka su a cikin marasa rinjaye. [5][6]

Manazarta gyara sashe

  1. "Adamawa seventh Assembly sets agenda for its operation". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2020-06-25.
  2. Ochetenwu, Jim (2019-06-13). "How Adamawa Assembly finally elected PDP member as Speaker". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-06-25.
  3. "Adamawa Assembly approves 40 new special advisers". P.M. News (in Turanci). 2019-10-22. Retrieved 2020-06-25.
  4. "Adamawa Assembly passes bill on free treatment of accident victims | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2017-11-28. Retrieved 2020-06-25.
  5. "After Supplementary Elections, PDP Snatches Majority Control At Adamawa Assembly From APC". Sahara Reporters. 2019-03-25. Retrieved 2020-06-25.
  6. "Adamawa Assembly polls: PDP wins 13, APC 11 seats". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-03-26. Retrieved 2020-06-25.