Majalisar Ƴancin ɗan Adam ta Kasa

Majalisar 'Yancin ɗan adam ta Kasa (NCHR). Kungiya ce ta kare hakkin dan adam ta kasar Masar da aka kafa a shekarar 2003 tare da manufar ingantawa da kiyaye' 'Yancin ɗan adam a Masar.[1] NCHR tana buga rahotanni na shekara-shekara game da matsayin haƙƙin ɗan adam a cikin ƙasar.[2] Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Boutros Boutros-Ghali ya taka muhimmiyar rawa wajen kirkirar kungiyar, kuma ya yi aiki a matsayin shugabanta har zuwa shekarar 2012.[3] A cikin shekarar dubu biyu da sha biyu 2012, a lokacin taƙaitaccen mulkin shekara guda na Muslim Brotherhood Hossam El Gheriany . [3] A cikin shekarar dubu biyu da Ashirin da daya (2021), bayan wa'adin mambobin NCHR ya ƙare, Majalisar Masar ta zabi Moushira Khattab don zama sabon shugaban NCHR don maye gurbin Fayek kuma Shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya amince da nadin ta da kuma sabon abun da ke cikin NCHR.

Majalisar Ƴancin ɗan Adam ta Kasa
Bayanai
Iri ma'aikata
Ƙasa Misra
Mulki
Hedkwata Kairo
Tarihi
Ƙirƙira 19 ga Yuni, 2003
nchregypt.org…

A yayin da NCHR take gudanar da ayyukanta da gashin kan ta, Cibiyar Nazarin Hakkokin Dan Adam ta Cairo, ta nuna kokwantonta dangane da hadin gwiwar NCHR da Majalisar Shura da kuma rawar da gwamnati ke takawa wajen zaben mambobin kungiyar.[4] A shekara ta 2009, Rahoton Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam a Masar, Sashin Kasar Amurka ta bayyana NCHR a matsayin 'wani bangare na shawarwari ga Majalisar Shura' amma ta amince da rahoton NCHR na 2008/2009 cewa tauye hakkin danAdam daga gwamnatin Masar, kamar sanya takunkumi na gaggawa, cin zarafin wadanda aka kulle, dokokin shawo kan ta'addanci marasa tasiri, da kuma takunkumi ga wasu jam'iyyu da Kungiyoyi masu zaman kan su (NGOs).[5]

A cikin shekara ta 2007, kungiyar ta zargi gwamnatin Masar da magudi a yayin zabe na kasar, tare da kungiyoyin adawa suna kira ga 'yan kasa da suyi kauracewa zaben. Kungiyar NCHR ta fitar da rahoton cewa gwamnatin kasar ta tilasta wa ma'aikata yin zabe kuma ta iyakance hanyoyin isa ga wuraren zabe ga masu lura. Gwamnatin Masar ta fitar da rahoton cewa kaso 75.9% sun zabi yin gyara ga kundin tsarin mulki na kasar, duk da cewa kawai kaso 27% na masu zabe ne suka kada kuri'unsu.[6]

A cikin shekara ta 2008, NCHR ta yi bincike akan abun da ya faru a Wurin Bauta na Saint Fana kuma ta bayyana rahoton da ya mayar da hankali akan bunkasar cin zarafi na bangaranci a kasar Masar.[7]

A binciken abun da ya farub bayan cisge tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak, wani kwamiti da ya hada da NCHR ta hada ta gano Mubarak, da tsohon ministan gida Habib el-Adly da wasu 'yan siyasa da nauyin mutuwar wasu 'yan zanga-zangan lumana a yayin tashin-tashin na ajiye aikin Mubarak.[8] Duk da haka, wannan rahoton ya fuskanci soke-soke musamman daga wadanda suke ganin a kama Mubarak a matsayin mai laifi, don sanya hannu a siyasance don ta'addanci ga masu zanga-zanga.[9] However, this report was met with criticism from those who believe that Mubarak should be held criminally, in addition to politically, responsible for violence against protesters[10]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Visions and Goals". National Council for Human Rights. Archived from the original on 3 March 2011. Retrieved 11 April 2011.
  2. "Annual Reports". National Council for Human Rights. Archived from the original on 3 March 2011. Retrieved 12 April 2011.
  3. 3.0 3.1 Who's who in Egypt's reshuffled Human Rights Council, Ahram Online, 4 September 2012.
  4. "Egypt National Council for Human Rights asserts its independence". National Human Rights Institutions Forum. Archived from the original on 19 July 2011. Retrieved 11 April 2011.
  5. "2009 Human Rights Report: Egypt". United States State Department. Archived from the original on 15 March 2010. Retrieved 12 April 2011.
  6. "Panel accuses Egyptian government of fraud in referendum". New York Times. 27 March 2007. Retrieved 12 April 2011.
  7. "National Council of Human Rights' report on Abū Fānā incidents: The incidents have unveiled the escalation of sectarian tension in Egypt". Arab-West Report translation of Al-Wafd newspaper, July 18, 2008. Retrieved 11 April 2011.
  8. "National Council of Human Rights' report on Abū Fānā incidents: The incidents have unveiled the escalation of sectarian tension in Egypt". Arab-West Report translation of Al-Wafd newspaper, July 18, 2008. Retrieved 11 April 2011.
  9. "Fact finding committee accuses Mubarak, Al-Adly of killing protestors". The Daily News Egypt. Archived from the original on 11 March 2012. Retrieved 12 April 2011.
  10. "Fact-finding committee slammed for not recommending trial of Mubarak". Almasry Alyoum, 27 March 2011. Retrieved 12 April 2011.