Maikanti Kachalla Baru (an haife shi a watan Yulib shekarar 1959 - 2020) injiniya ne kuma tsohon shugaban Hukumar Dillancin Mai ta Nijeriya. Ya riƙe muƙamin ne daga watan Yuli na shekarar 2016 zuwa watan Yuli na shekarar 2019. Baru memba ne a Hukumar Injiniyoyi ta Nijeriya. [1]

Maikanti Baru
Rayuwa
Haihuwa Misau, 1959
Mutuwa 29 Mayu 2020
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a

Rayuwarsa da karatunsa

gyara sashe

An haifi Baru a cikin Yulin shekarar 1959 a Misau, Jihar Bauchi. Yayi makarantar Kwalejin Gwamnatin Tarayya a Jos inda ya gama a shekarar 1978. Daga bisani ya wuce Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya inda ya samu digirin Injiniyanci a shekarar 1982. Har ilayau, Baru yana da digirin digir-gir akan kimiyyar injiniyanci ta komfuta wanda ya samu daga jami'ar Sussex dake a ƙsar Ingila..[2]

Aikin gwamnati

gyara sashe

Baru ya fara aikin gwamnati ne da wani kamfanin gidan rodi na Jos na kimanin shekara ukku daga shekarar 1988 zuwa shekarar 1991. A shekarar 1991 ne ya fara aiki da kamfanin mai na ƙasa NNPC a matsayin manajan injiniya. A kamfanin NNPC ya riƙe muƙamai da dama daga ciki harda Janaral Manaja na sashen Gas, muƙamin da ya riƙe daga shekarar 1997 zuwa shekarar 1999.

An naɗa Baru ne a matsayin babban Janaral Manaja na kamfanin NNPC a ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2016. Kuma yayi ritaya a ranar 7 ga watan Yuli na shekara 2019 bayan da aka naɗa Mele Kyari a matsayin sabon Janaral Manaja. [3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "10 things to know about new NNPC GMD, Maikanti Kacalla Baru". Premium Times. Retrieved 17 August 2019.
  2. "Maikanti Kacalla Baru". African Refiners Association. Archived from the original on 25 July 2019. Retrieved 21 August 2019. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)
  3. "Buhari appoints Mele Kyari as new NNPC GMD, seven COOs". Daily Trust. Archived from the original on 12 July 2019. Retrieved 21 August 2019. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)