Mahmoud El-Araby
Mahmoud El-Araby (an haife shi a shekara ta alif ɗari tara da talatin da biyu1932-Satumba 9, 2021) ɗan kasuwan Masar ne kuma mai tallafawa al'umma. Ya kafa ELARABY Group a shekarar 1964, kamfanin da ke kera da siyar da kayan aikin gida da kayan lantarki masu amfani a Masar da Gabas ta Tsakiya. [1] [2]
Mahmoud El-Araby | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Q12178000 , 1932 |
ƙasa |
Kingdom of Egypt (en) Republic of Egypt (en) United Arab Republic (en) Misra |
Mutuwa | 9 Satumba 2021 |
Makwanci | Q12178000 |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
Kyaututtuka |
gani
|
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Mahmoud El-Araby a shekara ta 1932 a Menoufia, Masar.
Sana'a
gyara sasheA shekarar 1974, El-Araby ya sami haƙƙin siyar da samfuran Toshiba. A shekarar Oktoba 1980, Toshiba ya amince da gina masana'anta a Benha don kera da kuma haɗa samfuran su. An kammala ginin Benha a shekarar 1982. An bi shi da babban rukunin Quesna wanda ke da masana'antu tara da masana'antu uku masu tallafi. Daga baya, El-Araby ya sami haƙƙin siyarwa da rarrabawa daga wasu kamfanoni, irin su Sharp, Hitachi, Seiko Watch Corp., Sony, da NEC.[3]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheYa haifi 'ya'ya maza shida da mata biyu.
Mutuwa
gyara sasheMahmoud El-Araby ya mutu a ranar 9 ga watan Satumba, 2021, yana da shekaru 89.[4] [5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "philanthropic industrialist" . Ahram Online . Retrieved 2022-05-19.Empty citation (help)
- ↑ "Egyptian business tycoon Mahmoud Al- Araby passes away at 89" . Egypt Today . 2021-09-09. Retrieved 2022-05-19.Empty citation (help)
- ↑ Okubo, Mami (2019-01-25). "El-Araby: Contributing to the Egypt-Japan relationship" . The Japan Times . Retrieved 2022-05-19.
- ↑ "Egypt Elaraby Group chairman dies at age 89" . Arab News . 2021-09-10. Retrieved 2022-05-19.
- ↑ "In Photos: Thousands attend funeral of business tycoon Mahmoud El-Araby in his hometown" . Ahram Online . Retrieved 2022-05-19.