Maharaja
Kalmar Mahārāja (kuma ana rubuta maharajah ) Sanskrit ne na "sarki mai girma" ko " babban sarki ". Yare da yawa na Indiya sun ari kalmar 'maharaja', a can yarukan sun haɗa da Punjabi, Bengali, Hindi da Gujarati. Ana amfani da shi galibi ga sarakunan Hindu ne. Nace mai sarauta ana kiran ta da suna Maharani (ko Maharanee ) ko kuma babbar sarauniya. Tana iya zama matar Maharaja ko mai mulki da kanta.
Maharaja | |
---|---|
position (en) da noble title (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | sarki |
Yarinya/yaro | Śanakanika Maharaja (en) |
Addini | Hinduism (en) |
Ƙasa | Indiya |
Applies to jurisdiction (en) | Indiya |
Dissolved, abolished or demolished date (en) | 5 Mayu 1948 |
Yadda ake kira mace | maharání da maharadžinja |
Burtaniya ta Indiya ta ƙunshi sama da jihohi 600 na mulkin mallaka kowannensu tare da mai mulkin ta. Wasu jihohin suna kiran mai mulkin Raja ko Thakur (idan mai mulkin Hindu ne ) ko Nawab (idan musulmi ne ); akwai wasu taken da yawa kuma. Asali masu mulkin manyan dauloli ne kawai kamar tsohuwar daular Gupta sune Maharajas amma a karnoni masu zuwa hatta shugabannin kananan masarautu suna amfani da taken. A cikin 1971, gwamnatin Indira Gandhi ta soke lakabi da kuɗi ga duk masu mulkin Indiya. Koyaya har yanzu wasu mutane suna da'awar irin waɗannan lakabi.