Mahamat Idriss
Mahamat Idriss (ne Koundja Ouya, an haifeshi ranar 17 ga watan Yuli, 1942 - ya rasu 3 ga watan Oktoban shekarar 1987) ya kasance ɗan wasan tsalle na ƙasar Chadi.
Mahamat Idriss | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Ndjamena, 17 ga Yuli, 1942 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Cadi Faransa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mutuwa | 3 Oktoba 1987 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Larabci Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | Dan wasan tsalle-tsalle | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 75 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 190 cm |
An haife shi ne a Fort-Lamy, Chadi, French Equatorial Africa.
Iyali
gyara sasheSana'a da Nasarori
gyara sasheKafin samun yancin Chadi a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 1960 ya wakilci Faransa, inda ya lashe gasar French National Championship a shekarar 1960 da 1961. [1] Ya kuma zama na goma sha biyu a wasannin Olympics na 1960 yayin da yake wakiltar Faransa. [2]
Ga Chadi ya zama na tara a wasannin Olympic na 1964. A kan Track and Field News cikin jerin zakarun wasannin tsalle da ake fitarwa shekara-shekara sunan Idriss ya fito a matsayin na tara a duniya cikin shekarar 1961, na goma a 1964 har wayau kuma dai na takwas a 1966.
Tsalle mafi tsawo na kansa da ya taɓa yi ya kasance mai tazarar mita 2.17, wanda ya samu damar yi a watan Afrilu 1966 a Fort-Lamy. Wannan har wayau wannan wata gagarumar nasara ce kuma abin tarihi ga Chadi, kodayake ya yi daidai da Paul Ngadjadoum da Mathias Ngadjadoum a shekarun 1993 da 1996 bi da bi.
Manazarta
gyara sashe- ↑ French Championships - GBR Athletics
- ↑ Men High Jump Olympic Games Rome 1960