Madonna ta Kyiv
Madonna ta Kyiv hoton wani tambari ne mai hoton wata mace da ke shayar da wani yaro wacce take rayuwa a tashar jirgin kasa na Kyiv domin kare kanta daga harin da sojojin Tarayyar Rasha suka kai a birnin Kyiv babban birnin Ukraine a shekarar 2022 . Hoton wanda wani dan jarida Andraş Földes ya dauka ya shahara a Intanet. Ya zamo misali na duka rikicin bil adama da yaƙi na rashin adalci. Hoton ya zamo abin ƙarfafa gwiwa wanda ake ajiye a Cocin Katolika da ke Mugnano di Napoli, kasar Italiya, wacce ta zamo alama ta fasaha dangane da juriya da kuma fatan nasara.[1]
Madonna ta Kyiv | ||||
---|---|---|---|---|
icon (en) da photography | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 26 ga Faburairu, 2022 | |||
Laƙabi | Мадонна Київська da Madonna of Kyiv | |||
Ƙasa | Ukraniya | |||
Nau'in | religious art (en) | |||
Mawallafi | András Földes (en) | |||
Ƙasa da aka fara | Ukraniya | |||
Ranar wallafa | 5 ga Maris, 2022 | |||
Inspired by (en) | Maryamu, mahaifiyar Yesu | |||
Depicts (en) | Maryamu, mahaifiyar Yesu | |||
Has cause (en) | Mamayewar Rasha na Ukraine na 2022 da Battle of Kyiv (en) | |||
Location of creation (en) | Kyiv Metro (en) | |||
Wuri | ||||
|
Madonna na Kyiv | |
---|---|
Fayil:Fecioara din Kiev resized.jpg | |
Mawaƙi | Marina Solomenikova |
Shekara | 2022 |
Wuri | Mugnano di Napoli |
Tarihi
gyara sasheA kwanakin farko na yakin Rasha a Ukraine, hoton Tatiana Blizhniak mai shekaru 27 da haihuwa wacce ke shayar da 'yarta Marichika mai watanni a duniya, wacce ta fake a ramukan jirgin kasa na Kyiv domin kare kanta daga harin daga harin bam wanda Sojojin Tarayyar Rasha suka kai a birnin Kiev, hakan ya janyo hankalin dan jarida na kasar Hungary András Földes, kuma ya dauki fim din a lokacin. Matar ta fake a kogon titin jirgin kasa tare da mijinta da yaronta daga ranar 25 ga Fabrairun shekarar, 2022. Duk da cewa a ranar 26 ga watan Fabrairu ya kamata a kwashe su, amma sun kasa fita daga tasahn da suke fake saboda yakin.[2] Hoton ya yadu har da shafukan yanar gizon Vatican ya watsa shi. Mawaƙin Ukrainian Marina Solomennikova daga Dnieper na daga cikin waɗanda suka ga faruwar al'amarin. Ya yi amfani da siffar wannan hoto na matan a matsayin hoton Maryamu tana reno jaririnta. A cikin hoton, an yi amfani da rigar wata mace 'yar Ukrain a matsayin mayafi na Maryamu, kuma an nuna kanta a gaban taswirar jirgin karkashin kasa. A ranar 5 ga Maris din shekarar 2020, mai zane ya sanya hoton da ya ƙirƙira akan Intanet.[3]
A matsayin roƙo ga firist na Jesuit Vyacheslav Oku, an aika kwafin zanen na hoton "Madonna daga Metro" zuwa Italiya don ajiye shi a wurin da malamin coci zai yi bauta.[1] A ranar Alhamis mai tsarki, Akbishop na Naples ya tsarkake zanen a matsayin abin bauta[4]. An nuna alamar a cikin Cocin Mai Tsarkin Zuciya na Yesu, wanda ake yi wa lakabi da "Madonna na Kiev", wanda ke cikin gundumar Munyano di Napoli. Fafaroma Francis ya keɓe alamar a ranar 25 ga Maris, 2022.[4]
Tatyana Blijniak daga bisani ya sami mafaka a Lviv.[5]
Muhimmanci
gyara sasheHoton ya zama wani tambari na rikicin bil adama da yakin rashin adalci, [5] kuma alama ce ta bege da juriya na mutanen kasar Ukrain.[1] Hoton, bi da bi, a matsayin mahaifiyar Yesu Banazare, wanda ya sami mafaka daga haɗarin Hirudus Mai Girma[6] a yau ana ɗaukarsa alama ce ta Maryamu ta zamani wadda ta sami mafaka daga tashin hankalin yaƙi kuma tana renon jaririnta kamarsa. .[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Toma, Mihai. ""Madonna of Kyiv". The picture of a Ukrainian woman breastfeeding her child in a subway shelter, became an icon in a church in Italy". libertatea.ro.
- ↑ https://www.puterea.ro/madona-del-metro-la-napoli/
- ↑ "Ukrainian mother breastfeeding during war becomes Marian icon". Aleteia.
- ↑ ""Madonna of Kyiv" icon depicted in one of the churches of Naples". risu.ua.
- ↑ "Our Lady of Kiev: Ukrainian nursing woman becomes a symbol of worship".
- ↑ Melnyczuk, Askold. "With Madonna in Kyiv". agnionline.bu.edu.