Madalla gari ne a Najeriya kusa da babban birnin tarayya Abuja. Yana tsakanin Suleja da Abuja kuma galibi ana kiransa da Abuja.

Madalla

Wuri
Map
 9°06′N 7°12′E / 9.1°N 7.2°E / 9.1; 7.2
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Madalla yana da wasu wuraren dake jan hankali kamar kewayen tsaunuka masu duwatsu da tsaunuka a ko'ina cikin garin. Wuri ne na ƙauye-birni mai yawan jama'a kusan 80,000.[1]

Hare-hare gyara sashe

A watan Satumban 2011 wasu ‘yan kabilar Igbo guda biyar wasu mutane biyu sun harbe su a wani harin da ake ganin na kabilanci.[1]

A can ne aka kai harin bom a ranar Kirsimeti na Disamba 2011 a cocin St. Theresa Catholic Church inda wata kungiyar ta’addanci da aka fi sani da Boko Haram ta kai hari.[2]

Har ila yau Madalla yana dauke da Dutsen Zuma ta wajen birnin.[3]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Oladipo, Adelowo (4 October 2011). "Igbo five: Peace returns to Madallah". Nigerian Tribune. Archived from the original on 6 January 2012. Retrieved 25 December 2011.
  2. "Nigeria rocked by church blasts". BBC News (in Turanci). 2011-12-25. Retrieved 2022-05-24.
  3. "Zuma Rock". Visit Nigeria Now (in Turanci). Archived from the original on 2022-06-27. Retrieved 2022-05-24.