M'Backé N'Diaye (an haife shi a shekarar 1994). ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Mauritaniya wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida ga ƙungiyar Nouakchott Kings da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mauritania.

M'Backé N'Diaye
Rayuwa
Haihuwa Rosso (en) Fassara, 19 Disamba 1994 (29 shekaru)
ƙasa Muritaniya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Aikin kulob/kungiya gyara sashe

N'Diaye yana taka leda a kulob din Super D1 Nouakchott Kings.[1]

Ayyukan kasa gyara sashe

Ya fara buga wasan kasa da kasa ne a ranar 3 ga watan Yunin 2021 a wasan sada zumunta da suka yi da Angola da ci 4-1.

A baya-bayan nan ya bayyana a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 da Equatorial Guinea a wasan da suka tashi 1-1 a ranar 16 ga Nuwamba.[2]

A ranar 19 ga watan Nuwamban 2021, N'Diaye ya kasance cikin tawagar karshe-23 a shiga gasar cin kofin Larabawa ta FIFA ta 2021 a Qatar.[3]

A ranar 3 ga watan Disamba, ya buga cikakken wasa da Hadaddiyar Daular Larabawa da ci 1-0.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. "MBACKÉ NDIAYE". ffrim.org. Retrieved 15 February 2022.
  2. "FIFA World Cup Qatar 2022™". www.fifa.com. Retrieved 2021-12-18.
  3. Coupe arabe de la FIFA: La liste de la Mauritanie connue". Africa Top Sports. Alfred Zikpi. 20 November 2021.
  4. "FIFA Arab Cup 2021™: Mauritania-United Arab Emirates". www.fifa.com. Retrieved 2021-12-18.