Luna Paiva
Luna Paiva (an haife ta a shekarar 1980). Ta kasance me aikin zane zane Wato da turanci (arts), ta shahara a duniya wajen zane kuma tana zaune a ƙasar Ajantina.
Luna Paiva | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa |
Argentina Faransa |
Sana'a | |
Sana'a | Mai sassakawa, painter (en) da mai daukar hoto |
Farkon Rayuwa
gyara sasheAn haifetane a garin Faris babban birnin Faransa, ita ɗiya ce game aikin ɗaukan hoto me suna Ronaldo paiva,anhaifeshi a shekarar alib 1942 zuwa shekarar 2003,ya rayu tsawon shekaru 61 a duniya, Sannan diyace ga fitacciyar me safaran aikin zane me suna Teresa Anchorena[1].
Karatu
gyara sasheta karanci ilimin tarihin Dan Adam da kimiyya da fasaha a jami'ar paris-sorbonne university,sannan ta karanci ilimin aikin fina finai a jami'ar new york[2].
Aiki
gyara sasheAyyukanta da yawa sun bayyana a matattaran ayuka na dindindin dake gidan tarihin Zane Wanda yake a Buenos Aires tun shekara ta alib 2012[3].Sannan kuma tayi wasu ayyuka na wucin gadi agarin Buenos Aires,Landan, Faris, new York city[4]
Rayuwar Iyali
gyara sashePaiva tanada yara guda biyu Iara da Romeo Wanda ta haifa da wani me aikin zane Wato (arts) Dan kasar Ajantina me suna Leandro Erlich. a shekarar 2021,ta Haifa yarinya me suna Athena Sol da wani dan kasar faransa me aikin zanen gine gine me suna Pablo Bofill Wanda ta aura a shekara ta alib 2022[5][6].
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.thejoyofplants.co.uk/introducing-luna-paiva%E2%80%99s-bronze-plant-sculptures
- ↑ https://objetdemotion.com/designer/luna-paiva/
- ↑ https://www.eggcollective-designingwomen.com/luna-paiva
- ↑ http://www.artnet.fr/artistes/luna-paiva/biographie
- ↑ https://www.eggcollective-designingwomen.com/luna-paiva
- ↑ https://www.revistavanityfair.es/articulos/boda-pablo-bofill-luna-paiva-la-fabrica