Luis Domingos Antonio Cazengue (an haife shi ranar 11, ga watan Agusta 1969), ana yi masa lakabi da Luizinho, tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola wanda ya fara aikinsa a Angola, kuma ya taka leda a Portugal.

Luizinho Luis
Rayuwa
Haihuwa Portuguese Angola, 11 ga Augusta, 1969 (55 shekaru)
ƙasa Angola
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Atlético Petróleos Luanda (en) Fassara1986-1992
Lusitano G.C. (en) Fassara1992-1993
C.D. Fátima (en) Fassara1993-1994
S.C. Braga (en) Fassara1995-1996262
  Académico de Viseu FC (en) Fassara1996-1998457
SC Lamego (en) Fassara1996-199762
  Angola men's national football team (en) Fassara1996-199610
Lusitânia F.C. (en) Fassara1999-2000293
F.C. Oliveira do Hospital (en) Fassara2001-2002120
SC Toronto (en) Fassara2002-2002102
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
lozinho

Sana'ar wasa

gyara sashe

Cazengue ya fara aikinsa tare da Atlético Petróleos de Luanda a Girabola. A lokacin da yake aiki tare da kulob ɗin Luanda ya lashe gasar Girabola sau biyar daga shekarun 1986 zuwa 1990, kuma ya lashe Taça de Angola a shekarun 1987, da 1992. A cikin shekarar 1992, ya tafi ƙasashen waje zuwa Portugal don komawa kulob ɗin Lusitano GC na Segunda Liga. A cikin shekarar 1993, ya yi aiki tare da kulob ɗin CD Fatima.[1] A kakar wasa ta gaba, ya sanya hannu tare a kulob ɗin SC Braga na Primeira Liga, inda ya bayyana a wasanni 26 kuma ya zira kwallaye biyu.[2] Bayan zamansa a Primeira Liga ya shafe lokaci tare da kulob ɗin SC Lamego, Académico de Viseu FC, Clube Caçadores das Taipas, Lusitânia FC, da FC Oliveira do Hospital. A cikin shekarar 2002, an ba da shi rancensa ga kungiyar kwallon kafa ta Toronto Supra na Canadian Professional Soccer League. Ya buga wasansa na farko a ranar 29 ga watan Agusta, 2002 a wasan da suka yi da Durham Flames, kuma ya ci kwallo a ci 5-2.[3] Abin takaici a lokacin da yake aiki tare da Toronto kulob din ya kare a karshe a Eastern Conference, kuma ya kasa samun damar shiga bayan kakar wasa.

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

An zabi Cazengue a matsayin dan wasan kwallon kafa na kasar Angola na gasar cin kofin kasashen Afirka na shekarar 1996. Ya fito a gasar da Afrika ta Kudu, inda Angola ta sha kashi da ci 1-0 a wasan.[4][5]

Girmamawa

gyara sashe
Petro Atlético
  • Girabola: 1986, 1987, 1988, 1989, 1990
  • Angola: 1987, 1992

Manazarta

gyara sashe
  1. "Luisinho" . Futebol 365 . Retrieved 2015-12-26.
  2. "ForaDeJogo.net - Luisinho (Luís Domingos António Cazengue)" . ForaDeJogo. Retrieved 2015-12-26.
  3. Glover, Robin. "August 29, 2002 CPSL Toronto Supra vs Durham Flames" . www.rocketrobinsoccerintoronto.com . Retrieved 2015-12-26.
  4. "South Africa - International Matches 1996-2000" . RSSSF . Retrieved 2015-12-26.
  5. Strack-Zimmermann, Benjamin. "Luisinho" . www.national-football-teams.com . Retrieved 2019-03-27.