Lubabatu Madaki tsohuwar jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood. Ta dade a masana'antar tana taka rawa a matsayin uwa.ta fito a shahararren fim din Nan Mai dogon zango na Tashar Arewa 24 Mai suna DADIN KOWA.[1]

Takaitaccen Tarihin ta

gyara sashe

Jarumar an haifeta a unguwan kofan mata a Jihar Kano a ranar 18 ga watan oktoba a shekarar 1973,tayi karatun firamare da na islama a unguwar Shahuci a Kano,tayi aure tana da shekaru 29 inda tayi zaman auren na iyakacin wata tara auren ya mutu. Ta kara Wani auren inda ta haifi Yara guda biyu mace da namiji, ta Kara Wani auren na uku da wancan ya mutu,a yanzun haka tana da jikoki guda uku a duniya,ta shigo masana'antar kanniwud a shekarar 1995,fim din daya daukaka ta shine fim din MAI RABO sekuma fim ɗin DAN ALMAJIRI, tati fina finai da dama Wanda Basu kirgo a masana' antar tare da tsofaffin jarumai a masana'antar.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bbc.com/hausa/media-59880795
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-26. Retrieved 2023-07-26.