Lovisa Tuyakula Mulunga (an haife ta a ranar 18 ga watan Maris 1995) 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce ta kasar Namibia wacce ta yi karatu a Jami'ar Jihar Albany kuma tana taka leda a matsayin mai tsaron gida ga kulob ɗin Golden Rams, da kuma ƙungiyar ƙasa ta Namibia, wacce kuma aka sani da Brave Gladiators.[1] An nada ta 2011/2012 Namibia Women's Super League Player of the Season.[2] [3]

Lovisa Mulunga
Rayuwa
Haihuwa Windhoek, 18 ga Maris, 1995 (29 shekaru)
ƙasa Namibiya
Karatu
Makaranta Albany State University (en) Fassara
University of Namibia (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Albany State Golden Rams women's soccer (en) Fassara-
  Kungiyar Kwallon Kafa ta Mata ta Namibiya-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
hutun lovisa mulunga

Mulunga ta lashe gasar NFA Women Super League tare da kulob ɗin JS Academy kuma tana cikin tawagar 'yan kasa da shekaru 20 Zone 6 da suka lashe kofin NFA/DFB Women Super Cup na farko a 2012 bayan da ta doke Brigade United 21 da ci 8-0.[4] Mulunga, ita ce kyaftin din kungiyar mata ta kasa da kasa ‘yan kasa da shekaru 17, kuma ta buga wa kungiyar ‘yan kasa da shekaru 20 wasa. [5]

Mulunga ana daukarta a matsayin ƙwararriyar 'yar wasa. Ta kasance memba a cikin manyan 'yan wasan kasar da suka taka leda a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin mata na Afirka ta shekarar 2012.

Manazarta

gyara sashe
  1. Nandjigwa, Gabriel (18 February 2013). " "The Rock" expectant of new season" . The Villager. Retrieved 10 October 2016.
  2. "Mulunga Best Player as Academy wins Super League" . Namibia Football Association. 6 August 2012. Retrieved 10 October 2016.
  3. "Mulunga, JS Academy win titles" . The Namibian. 7 August 2012. Retrieved 10 October 2016.
  4. "Zone VI team are Super Cup Champs" . Namibia Football Association. 12 November 2012. Retrieved 10 October 2016.
  5. "Mulunga back to lead" . Namibia Football Association. 1 February 2012. Retrieved 25 October 2016.Empty citation (help)

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe