Livingstone Mqotsi
Livingstone Mqotsi (18, Afrilu 1921–25, Satumba 2009), wanda kuma aka sani da Livy, ya kasance sanannen mutum a Afirka ta Kudu, musamman a fannin ilimin halin ɗan adam da gwagwarmaya. An haife shi a cikin iyali mai ƙarancin kuɗi, ya nemi ilimi da fafutuka. Tafiyar karatunsa sa kai shi ne Jami'ar Fort Hare, a kasar Afirka ta Kadu, inda ya karanta ilimin zamantakewar al'umma kuma ya yi zama ɗaya daga cikin fitattun ɗaliban Monica Wilson. Ya tsunduma cikin fafutuka da tsayin daka wajen yakar wariyar launin fata kuma ya shahara wajen hada al'umma.
Livingstone Mqotsi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Keiskammahoek (en) , 18 ga Afirilu, 1921 |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Mutuwa | 25 Satumba 2009 |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Fort Hare |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, Malami da social anthropologist (en) |
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.