Lampese gari ne, a ƙaramar hukumar Akoko Edo a cikin Jihar Edo, Najeriya, wanda ke kan titin Ibillo zuwa Abuja. Garin dai kofa ce ta hanyar Afemai da jihar Edo daga yankin Kogi, domin gari ne mai iyaka tsakanin jihar Edo da jihar Kogi.