Laetitia Rispel
Laetitia Charmaine Rispel Farfesa ce ta Afirka ta Kudu a fannin Kiwon Lafiyar Jama'a a Jami'ar Witwatersrand. Ayyukan Rispel sun binciki manufofin kiwon lafiya da gudanarwa da bincike na ayyukan kiwon lafiya.
Laetitia Rispel | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Witwatersrand |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da public health (en) |
Employers | Jami'ar Witwatersrand |
Kyaututtuka |
Sana'a da tasiri
gyara sasheRispel ta yi aiki a jere a matsayin shugabar Sashen Lafiya na Gauteng (daga shekarun 2001), Kwamitin Binciken Kimiyya na ɗan Adam na Afirka ta Kudu (Human Sciences Research Council of South Africa HIV/AIDS) shirin binciken HIV/AIDS (daga shekara ta 2006) da Jami'ar Witwatersrand Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a (daga shekara ta 2012).[1][2][3] Daga shekarun 2008 - 2014 ta kasance shugabar kungiyar kula da lafiyar jama'a ta Afirka ta Kudu.[4] Ta riƙe Cibiyar Bincike ta Kasa na Cibiyar Nazarin Afirka ta Kudu akan Ma'aikatan Lafiya da Daidaituwa, da Inganci kuma a cikin shekarar 2016 an zaɓe ta a matsayin mataimakiyar shugaban da aka zaɓa na Ƙungiyar Lafiya ta Duniya.[3] Rispel ta kasance shugabar kungiyar kula da lafiyar jama'a ta duniya tun daga shekarar 2018, kuma ita ce mace ta farko a Afirka da ta riƙe wannan muƙamin.[5][6] Ita memba ce a Kwalejin Kimiyya ta Afirka ta Kudu.[7]
Kyaututtuka da karramawa
gyara sashe- Shoprite Checkers/SABC2 Kyautar Mata ta Shekara ta Rukunin Lafiya, (2003)[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Shoprite Holdings | Woman of the year 2003 announced". Retrieved 2017-10-15.
- ↑ Staff Reporter. "New head for HIV/Aids research at HSRC". The M&G Online (in Turanci). Retrieved 2017-10-15.
- ↑ 3.0 3.1 Advertorial. "Celebrating women of excellence in research: NRF SA Research Chairs Initiative". The M&G Online (in Turanci). Retrieved 2017-10-15.
- ↑ "Prof Laetitia Rispel voted VP / President elect of the WFPHA | Public Health Association of South Africa". www.phasa.org.za (in Turanci). Retrieved 2017-10-15.[permanent dead link]
- ↑ "2019 - World Federation of Public Health Associations". www.wfpha.org. Retrieved 2019-06-26.
- ↑ "2018-05 - Wits Research Chair is first African president of global public health association - Wits University". www.wits.ac.za. Retrieved 2019-06-26.
- ↑ "Members". www.assaf.org.za (in Turanci). Retrieved 2017-10-15.