Laetitia Nyinawamwiza
Laetitia Nyinawamwiza (an haife ta a shekara ta 1972) Malama ce kuma 'yar siyasa ta ƙasar Ruwanda. Ta riƙe muƙaman gudanarwa na ilimi da yawa, kuma tun daga shekarar 2019 ta zama memba a Majalisar Dattawa ta Ruwanda, mai wakiltar lardin Arewa. [1]
Laetitia Nyinawamwiza | |||
---|---|---|---|
2019 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 17 Disamba 1972 (52 shekaru) | ||
ƙasa | Ruwanda | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, Malami da senior lecturer (en) |
Rayuwa
gyara sasheLaetitia Nyawamwiza tana da digirin digirgir a fannin samar da dabbobi (kiwo). Daga shekarun 2009 zuwa 2011 ta kasance Shugabar Sashen Haɓaka Dabbobi a Tsangayar Aikin Noma a Jami'ar Ƙasa ta Ruwanda, kuma a cikin shekara ta 2010 ta zama Babbar Malama a Kwalejin Aikin Noma. Daga shekarun 2011 zuwa 2013 ta kasance mataimakiyar shugabar kula da harkokin ilimi da bincike a babbar jami'a. Cibiyar Noma da Kiwon Dabbobi, ISAE-Busogo. Daga shekarun 2012 zuwa 2013 ta kasance Ag. Rector a ISAE-Busogo. [1]
A watan Oktoba 2013 Shugaba Kagame ya naɗa ta a matsayin shugabar Kwalejin Aikin Gona, Kimiyyar Dabbobi da Magungunan Dabbobi. [2] A shekarar 2018 ta mayar da martani ga korafe-korafen ɗalibai na rashin samar da ababen more rayuwa a kwalejin, inda ta amince da matsalar sannan ta ce kwalejin ta roki gwamnati da ta taimaka musu da kuɗi. [3]
Daga shekarun 2012 zuwa 2019 Nyinawamwiza ta kasance memba a kwamitin gudanarwa na majalisar ilimi ta ƙasa ta Rwanda. Daga shekarun 2013 zuwa 2015 Nyinawamwiza ta kasance mamba a kwamitin tantancewa na majalisar ilimi ta gabashin Afirka. Ta kasance mataimakiyar shugaban kwamitin gudanarwa na Cibiyar Nazarin Kimiyyar Kimiyya (INES-Ruhengeri) daga shekarun 2012 zuwa 2019, kuma mataimakiyar shugaban kwamitin gudanarwa na Hukumar Bincike da Ci Gaban Masana'antu ta Ƙasa (NIRDA) daga shekarun 2016 zuwa 2019. [1]
Daga shekarun 2018 zuwa 2019 Nyinawamwiza ta kasance a cikin kwamitin gudanarwa na Ruwanda Mountain Tea, [1] manajan Rubaya Nyabihu Tea Company Ltd da Kitabi Tea Company Ltd. [4]
A shekara ta 2019 Nyinawamwiza na ɗaya daga cikin 'yan takara biyu da aka zabta a matsayin Sanata mai wakiltar Lardin Arewa. [5] A watan Nuwamba 2019, da take magana a gundumar Musanze, ta yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa 'ya'yansu sun shagaltar da su a lokacin hutun makaranta. [6]
Kyauta
gyara sasheNyinawamwiza ta lashe lambar yabo ta mata mafi tasiri a Afirka a fannin kasuwanci da gwamnati a babbar lambar yabo ta Global Africa Awards 2017. [7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Senators Profiles: Details Archived 2020-10-26 at the Wayback Machine, parliament.gov.rw. Accessed May 5, 2020.
- ↑ Eugène Kwibuka, Profile: Who is who at University of Rwanda, The New Times, October 17, 2013.
- ↑ Jean d'Amour Mbonyinshuti, Science students decry insufficient infrastructure, The New Times, February 15, 2018.
- ↑ Daniel Sabiiti, Here Are New Senators Taking Oath Today, The New Times, October 17, 2019.
- ↑ Nasra Bishumba, Men dominate senatorial provincial seats, The New Times, September 17, 2019. Accessed May 5, 2020.
- ↑ Régis Umurengezi, School holidays: Parents urged to stay closer to children, The New Times, November 11, 2019. Accessed May 5, 2020.
- ↑ Celebrating Rwandan Women of 2018, KT Press, March 7, 2018. Accessed May 5, 2020.