Labarin Dajjal da saukowar Annabi Isah (A.S) 1

🪨🪨🪨

LABARIN DUJJAL DA SAUKOWAR ANNABI ISAH (AS) (1)

Annabi صلى الله عليه وسلم ya tsoratar da al'ummarsa game da dujjal ya kuma siffanta shi siffantawar da babu wani annabi gabaninsa da ya siffanta shi kamar haka har sahabbai suka tsorata suka za ci ko yana cikin wasu gonakin dabino da ke kusa. Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce musu: "In Dujjal zai fito ina tare da ku to, ni ne zan yi jayayya da shi ba ku ba, idan kuma ya fito bana tare da ku to, kowannenku shi zai kare kansa, Allah سبحانه وتعالى shi ne khalifana a kan kowane musulmi."

Annabi صلى الله عليه وسلم ya bayar da labarin dujjal kamar haka:

"Tsakanin halittar Annabi Adam عليه السلام zuwa tashin alkiyama ba a yi wani al'amari mafi girma kamar Dujjal ba, kowane annabi sai da ya gargadi mutanensa game da wannan makaryacin mai ido daya.

Dujjal matashi ne mai dukunkunannen gashi, idonsa daya kamar busasshen inibi yake. Lalle shi mai ido daya ne, Ubangijinku kuma ba mai ido daya ba ne, zan iya kamanta shi da Abdul Uzza bn Qatan an rubuta a tsakanin idanunsa 'kafir'.

A tare da shi akwai ruwa da wuta. Abin da mutane suke ganinsa ruwa to wuta ce mai kona wa. Abin kuma da mutane suke ganinsa wuta to, ruwa ne mai dadi da sanyi. Duk wanda ya gamu da shi a cikinku ya fada cikin abin abin da yake ganinsa wuta, hakika shi ruwa ne mai dadi.

Dujjal zai fito ta wata hanya tsakanin kasar Sham da Iraki zai watsa barna dama da hagu, zai shiga kowane gari amma ban da Makkah da Madina, domin babu wata kubba a cikin wadannan birane face sai mala'iku sun yi sahu a kansu suna gadinsu, saboda haka mutane za su gudu cikin duwatsu saboda tsoron Dujjal.

Ya bayin Allah! "Ku tabbata a kan dugadiginku"! Sahabbai suka ce: "Ya Rasulallah, tsawon wane lokaci zai zauna a ban kasa"? Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Kwana ar'bain. Wani yininsa zai kasance kamar tsawon shekara, wani kamar tsawon wata, wani kuma yinin kamar sati. Sauran kwanakinsa za su kasance kamar tsawon yinin ku". Sahabbai suka ce: "Ya Rasulallah! Wannan ranar da za ta yi tsawo kamar shekara zai isar mana mu yi salloli biyar a cikinsa? Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "A'a, ku dinga dai kintatar lokaci". Sahabbai suka sake tambaya suka ce: "Ya Rasulallah! Yaya saurinsa yake a ban kasa"? Ya ce: "Kamar hadari ne wanda iska ta kado shi." ....

Manazarta

gyara sashe

                     الله تعالى اعلم