Labaran gargajiya game da tarihin LGBT a kasashen Afurka

 

Labaran gargajiya game da tarihin LGBT a kasashen Afurka
LGBT themes in mythology (en) Fassara

Jigogi daban-daban na LGBT suna nan a cikin tatsuniyoyin Afirka da dama, na farko daga cikinsu shine Voodoo.

 

 
Zanen Baron Samedi, loa mai sha'awar jinsuna biyu

Akwai ruhohi ko alloli da dama da suke wanzuwa a Haitian da Louisiana Voodoo da ake kira loa (ko lwa ). Ana iya danaganta waɗannan loa azaman dangin mutane ko kuma daidaikun mutane da ke da alaƙa ta hanyoyi iri-iri, wanda ke da alaƙa da wasu fannonin rayuwa.

Wasu daga cikin mutanen lwa suna da alaƙa ta musamman da sihiri, bautar kakanni ko mutattu kamar Ghedes da Barons. Yawancin waɗannan suna da alaƙa ta musamman da sauya jinsi ko jima'i tsakanin jinsi guda. [1] Waɗannan sun haɗa da Ghede Nibo, ruhun dake kula da waɗanda suka mutu suna ƙanana. Wani lokaci ana daukar shi a matsayin mata-maza mai jawo hankalin wadanda ya mallake wajen saduwa da kowane irin jinsi, musamman ma masu sauya jinsi ko kuma mace mai halayen 'yan madigo. [2] Iyayen Ghede Nibo sune Baron Samedi da Maman Brigitte; Baron Samedi shi ne shugaban Ghedes da Barons kuma ana siffanta shi da mutum mai son kwalliya kuma dan luwadi/madigo ko a wasu lokutan a matsayin dan/'yar-daudu, sanye da babban hula da riga tare da siket na mata da takalma. Samedi yana da ɗabi'ar "jawo sha'awa" waɗanda ke ketare iyakokin jinsi kuma suna nuna sha'awar jima'i ta dubura. [3]

Sauran Barons da ke nuna halayen 'yan luwadi su ne Baron Lundy da Baron Limba, wadanda masoya ne kuma suna koyar da wani nau'in kokawa na tsiraici a makarantun su, wanda aka yi imanin yana kara karfin sihiri. [4] Baron Oua Oua, wanda sau da yawa yakan bayyana da siffa na yara, ana kiransa baron "mafi kusanci da luwadi" na daga Voodoo. [5]

Wani lwa, Erzulie, yana da alaƙa da ƙauna, sha'awa da kyau. Erzulie na iya bayyana halaye da ke da alaƙa da LGBT, gami daudunci ko halayen mutanen amazon, gami da yanayin mata na al'ada. Lokacin zama jikin maza, waɗannan abubuwan na iya haifar da daudunci ko kuma ɗabi'ar luwaɗi, alhali suna iya haifar da madigo ko kyamar namiji a cikin mata. Ana kallon Erzulie Freda a matsayin mai kare 'yan luwadi, kuma Erzulie Dantor yana da alaƙa da 'yan madigo. [6]

Santerria da Candomblé

gyara sashe

Santería da Candomblé addinai ne da dama waɗanda aka samo daga akidar mutanen yankin Yarbawa da mabiya Katolika, waɗanda suka fi yawa a Kudancin Amirka, gami da Cuba da Brazil. Tatsuniyoyinsu suna da kamanceceniya da dama da mutanen Yarbawa, kuma sun ƙunshi wurin tarihi na Orishas (ruhohi), kwatankwacin (kuma galibi ana gano su da) loa na Voodoo.

A cikin wani Cuban Santería "pataki", ko labarin tatsuniya, an yaudare uwargijiyar teku Yemaha cikin jima'i da ɗanta Shango. Don boye kunyar ta dangane da wannan al'amari, ta kori sauran ’ya’yanta guda biyu, Inle da Abbata, su zauna a gindin teku, tare da yanke harshen Inle da kuma maida Abbata kurma. Sakamakon keɓewarsu da kaɗaicin da suka yi, Inle da Abbata sun zama abokai masu sha'awar juna sannan kuma masoya, suna iya yin magana cikin nutsuwa. Ana amfani da wannan pataki don bayyana asalin lalata tsakanin 'yanuwa na kusa, bebe, da kurma danagane da nuna luwadi. [7]

Duba kuma

gyara sashe

 

  • Jigogi na LGBT a cikin tatsuniyoyi
  • Batutuwan LGBT da Afro-Amurka a cikin Amurka
  • Tauhidin Queer
  • Addini da luwadi
  • Addini da transgenderism

Manazarta

gyara sashe
Musamman
  1. Conner & Sparks (1998), p. 157, "Ghede"
  2. Conner & Sparks (1998), p. 157, "Ghede Nibo"
  3. Conner & Sparks (1998), p. 83, "Baron Samedi"
  4. Conner & Sparks (1998), p. 83, "Baron Limba" & "Baron Lundy"
  5. Conner & Sparks (1998), p. 83, "Baron Oua Oua"
  6. Conner & Sparks (1998), p. 135, "Erzulie"
  7. Conner & Sparks (1998), p. 39, "Abbata"

Gabaɗaya

gyara sashe
  •  
  •  

Kara karantawa

gyara sashe
  •  
  •  
  •  

Samfuri:LGBT fiction