Kwale-kwalen Dufuna
Kwale-Kwalen Dufuna wani Kwale-Kwale ne da wani makiyayi (Bafulatani) ya gano shi a shekarar Alif da dari tara da tamanin da bakwai (1987),[1] mai tazarar kilomita kaɗan daga ƙauyen Dufuna da ke a Ƙaramar Hukumar Fune, nesa kaɗan da kogin Komadugu Gana, a jihar Yobe, da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya.[2][3]
Tarihi
gyara sasheA ranar 4 ga watan Mayun (1987), wani makiyayi (Bafulatani) mai suna Malam Ya'u a yayin da yake tona rijiya ya gano wannan Kwale-Kwalen. Nan da nan kuma sai ya yi hanzari ya sanar da sarkin ƙauyensu game da lamarin. [4]
A cikin shekara ta 1989 da 1990, Jami'ar Maiduguri ta fara binciken wurin don tabbatar da ko Kwale-Kwale ne.
Jami'ar Frankfurt da ta Maiduguri wadda Farfesa Peter Breunig da Garba Abubakar, suka gudanar da binciken wurin, in da kuma aka sake ɗaukar samfurin Kwale-kwalen da wasu sassa domin aiwatar da gwaje-gwaje a Jamus a karo na biyu.
A shekara ta Alif da Ɗari Tara da Casa'in da Huɗu (1994), wata tawagar binciken kayan tarihi daga Jamus da Najeriya ta tona wurin, in da ma'aikata Hamsin sukayi aikin haƙo Kwale-Kwalen, wadda hakan ya ɗauke su sama da mako biyu, kuma an gano tsawonsa ya kai mita 8.4, faɗinsa kuma mita 0.5 sannan yana da kauri 5cm.
An gano Kwale-kwalen a cikin wani ruwa da aka tona da yumɓu ke kwance tsakaninsa da bisa wanda ke kare shi a cikin yanayi mara amfani da iskar oxygen.
Kwale-kwalen wanda ya kasance sananne kuma mafi tsufa a nahiyar Afirka, sannan na biyu a tsufa a duniya. An haƙiƙance kan cewar yakai tsakanin shekaru 8,000 zuwa 8,500 kafin haihuwar Annabi Isa (AS).
Wataƙila an ƙirƙire shi a cikin al'adar yin kwale-kwale a wancan lokacin, kuma an yi amfani da shi wajen kamun kifi a gefen kogin Komadugu Gana. Wataƙila jama'a ne suka ƙera shi daga yankin Yammacin Sahara, zuwa kogin Nilu na tsakiyar Sudan, zuwa yankin Arewa na Kenya.[5]
A yanzu haka dai, Kwale-kwalen yana cikin gidan Adana Kayan Tarihi na Damaturu a jihar Yobe, Najeriya.
A ranar Huɗu ga watan Mayun Alif da Ɗari Tara da Tamanin da Bakwai (1987), wani makiyayi (Bafulatani) mai suna Malam Ya'u a yayin da yake tona rijiya.
Nan dai ya yi hanzari ya sanar da sarkin ƙauyensa game da lamarin.
A cikin shekara ta 1989 da 1990, Jami'ar Maiduguri ta fara binciken wurin don tabbatar da ko Kwale-Kwale ne.
Jami'ar Frankfurt da na Maiduguri wadda Farfesa Peter Breunig da Garba Abubakar, suka gudanar da binciken wurin, in da kuma aka sake ɗaukar samfurin Kwale-kwalen da wasu sassa domin aiwatar da gwaje-gwaje a Jamus a karo na biyu.
A shekara ta Alif da Ɗari Tara da Casa'in da Huɗu (1994), wata tawagar binciken kayan tarihi daga Jamus da Najeriya ta tono wurin, in da ma'aikata Hamsin suka haƙo in da ake zargin Kwale-Kwalen yake wadda ya ɗauke su sama da mako biyu, kuma an gano tsawonsa ya kai mita 8.4, faɗinsa mita 0.5 da kauri 5cm.
An gano Kwale-kwalen a cikin wani ruwa da aka tona da yumɓu ke kwance tsakaninsa da bisa wanda ke kare shi a cikin yanayi mara amfani da iskar oxygen.
Kwale-kwalen wanda ya kasance sanannen kuma mafi tsufa a nahiyar Afirka, sannan na biyu a tsufa a duniya. An haƙƙace kan cewar ya kai tsakanin shekaru 8,000 zuwa 8,500 kafin haihuwar Annabi Isa AS.
Wataƙila an ƙirƙire shi a cikin al'adar yin kwale-kwale a wancan lokacin, kuma an yi amfani da shi wajen kamun kifi a gefen kogin Komadugu Gana.
Wataƙila jama'a ne suka ƙera shi daga yankin Yammacin Sahara, zuwa kogin Nilu na tsakiyar Sudan, zuwa yankin Arewa na Kenya.
A yanzu haka dai, Kwale-kwalen yana cikin gidan Adana Kayan Tarihi na Damaturu a jihar Yobe, Najeriya.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.academia.edu/6747300/New_research_on_the_Holocene_settlement_and_environment_of_the_Chad_Basin_in_Nigeria
- ↑ https://www.sciencedirect.com/science/article/abs/pii/S1040618203000144
- ↑ https://books.google.com.ng/books?id=TL1q6BiISt8C&pg=PT2640&redir_esc=y
- ↑ https://www.academia.edu/35514815/DUFUNA_CANOE_FIND_BIRTHING_THE_UNDERWATER_CULTURAL_HERITAGE_IN_NIGERIA
- ↑ https://www.nigeriagalleria.com/Nigeria/States_Nigeria/Yobe/Dufuna-Canoe-Yobe.html