Kurfi Umaru

Dan siyasar Nigeria

Kurfi Umaru (an haife shi a shekarar dubu daya da dari tara da hamsin da biyu 1952) a kurfi, jihar katsina. memba ne a jam'iyyar APC kuma ya kasance Sanata a majalisar dokoki ta Najeriya har zuwa watan Mayun shekarar 2019. Umaru ya samu ilimi ne a Najeriya amma ya halarci wani lokacin bazara a Jami'ar Jihar Kansas a Amurka. Ya wakilci Katsina Central. An kayar dashi a matakin farko na APC.[1][2]

Kurfi Umaru
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - Mayu 2019
Ahmed Sani Stores - Kabir Ɓarkiya
District: Katsina Central
Rayuwa
Haihuwa 1952 (71/72 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Farkon Rayuwa gyara sashe

An haifeshi a karamar hukumar Kurfi dake Jihar Katsina a shekarar 1952. Dan siyasa ne a jamiyar APC wanda yayi matsayin dan majalisar dokoki na jiha[3].


Ilimi gyara sashe

Bayan yasamu damar kammala karatunsa na farko, ya fara zuwa Kwalejin Malamai na Katsina, inda daga nan ya wuce zuwa makarantar horar da malamai. Bayan ya yi koyarwa a matsayin malami har tsawon shekara guda, sai ya ci gaba da zuwa Babbar Kwalejin Malamai, a Kano, inda ya sami takardar shedar karatu ta Ilimin Ƙasa (NCE).[4]

Kurfi na daga cikin membobin kungiyar United Nigeria Peoples Congress (UNPC).[4]

Manazarta gyara sashe

  1. "Katsina Senator, Kurfi, Loses APC Primary". Thisdaylive. 2018-10-04. Retrieved 2020-01-08.
  2. Ebhota, Eseohe (2018-10-04). "Katsina: Sen Kurfi, first casualty of APC primaries – Daily Trust". Dailytrust.com.ng. Archived from the original on 2019-02-13. Retrieved 2020-01-08.
  3. https://worddisk.com/wiki/Kurfi_Umaru/[permanent dead link]
  4. 4.0 4.1 "Senator Umaru Ibrahim Tsauri". Peoples Democratic Party of Nigeria. 2018-10-04. Archived from the original on 2021-05-06. Retrieved 2020-01-08.