Kur Kur
Kur Gai Kur (an haife shi a ranar 20 ga watan Fabrairu 2000) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Sudan ta Kudu wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya ga ƙungiyar South Macedonia ta Rabotnički da ƙungiyar ƙasa ta Sudan ta Kudu.[1]
Kur Kur | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Mombasa, 20 ga Faburairu, 2000 (24 shekaru) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Aikin kulob
gyara sasheAn haifi Kur a sansanin gudun hijirar Sudan ta Kudu a Kenya, kuma ya koma Australia yana da shekaru 2. Ya fara buga kwallon kafa da Modbury Vista tun yana dan shekara 8 zuwa 9, kafin ya shiga shirin Skillaroos har ya kai shekaru 16. Daga nan ya rattaba hannu kan Modbury kafin shiga cikin Croydon King a shekarar 2020. Ya koma Adelaide City a shekarar 2021, inda ya fara babban aikinsa. [2]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheKur ya fara buga wasansa na farko tare da tawagar kasar Sudan ta Kudu a wasan sada zumunci da suka yi rashin nasara a hannun Jordan da ci 2-1 a ranar 31 ga watan Janairun 2022. [3]