Kpalikpakpa zã ko Bikin Kpalikpakpa biki ne na shekara-shekara da sarakuna da jama'ar yankin gargajiya na Kpalime ke yi a yankin Volta na Ghana. An samo sunan bikin ne daga wani kira a cikin Ewe wanda shine "Kpalikpakpa si tu makpata" ma'ana "harbi ba tare da yin rikodi ba". Ana nufin bikin ne don tunatar da mutanen Kpalime jajircewar kakanninsu a lokacin yake-yake a zamanin da.[1]

Infotaula d'esdevenimentKpalikpakpa zã
Iri biki
Wuri Kpalime Traditional Area (en) Fassara
Yankin Volta, Yankin Volta
Ƙasa Ghana
Nahiya Afirka

Farkon gudanar bikin gyara sashe

An fara gudanar da bikin ne a watan Nuwamban shekarar 1997 kuma tun daga lokacin ake gudanar da bikin duk shekara. Babban shugaban yankin a lokacin shine Togbega Asio XI na Kpale. Bikin farko ya kasance a Wegbe Kpalime. Tun daga wannan lokacin ake juya shi tsakanin garuruwan gundumar.[1] An gudanar da bikin na takwas a Kpale a watan Nuwamba 2004.[2] An yi bikin bukin karo na 17 a watan Nuwamba 2012 a Kaira.[3]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Kpalime Celebrate Kpalikpakpa Festival". Ghana Home Page. 1997-11-05. Retrieved 2011-09-17.
  2. "Chiefs and people of Kpalime launch festival". Ghana Home Page. 2004-10-11. Retrieved 2011-09-17.
  3. "Kaira Hosts 17th Annual KPALIKPAKPA ZÃ (Festival)". Kpalimegh.netii.net. Archived from the original on 27 December 2013. Retrieved 30 January 2013.