Kodjovi Mawuéna
Kodjovi Mawuéna (an haife shi ranar 31 ga watan Disamba 1959) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Togo kuma koci.
Kodjovi Mawuéna | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Tsévié (en) , 31 Disamba 1959 (64 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Togo | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya |
Aikin kulob
gyara sasheAn haife shi a Tsévié, Mawuéna ya buga wasan ƙwallon ƙafa a cikin wasannin gida.
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheMawuéna ya buga wa tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo, gami da wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA guda ɗaya. Ya zama kyaftin din Togo a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1984.[1]
Aiki a matsayin manaja
gyara sasheBayan ya yi ritaya daga wasa, Mawuéna ya zama manaja. Ya jagoranci kulob na gida da yawa, ciki har da OC Agaza. A cikin shekarar 2004, an nada shi kocin na shekara yayin da yake sarrafa Dynamic Togolais. [2]
Mawuéna ya kasance mataimakin koci na kungiyar kwallon kafa ta kasar Togo kuma ya zama koci na riko a lokacin da Gottlieb Göller ya fice a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara ta 2000. An kuma nada shi a matsayin kocin riko na Togo a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006 lokacin da Otto Pfister da Piet Hamberg suka bar mukamansu.
Manazarta
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Kodjovi Mawuéna – FIFA competition record