Kiyomizu Temple
Kiyomizu Temple wajen bautar Buddhizanci da ke birnin Kyoto, kasar Japan. Wurin bautar na daga cikin wuraren tarihi na tsohuwar Kyoto (biranen Kyoto, Uji da kuma Otsu) na UNESCO.[1]
Kiyomizu Temple | |
---|---|
清水寺 | |
UNESCO World Heritage Site | |
Historic Monuments of Ancient Kyoto Saigoku Kannon Pilgrimage The Twenty-Fifth Reikyo of Dharan Shonin [[]] Shinbutsu Reijō Junpai no Michi | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Japan |
Prefecture of Japan (en) | Kyoto Prefecture (en) |
City designated by government ordinance (en) | Kyoto |
Ward of Japan (en) | Higashiyama-ku (en) |
Coordinates | 34°59′41″N 135°47′06″E / 34.994831°N 135.785003°E |
History and use | |
Renovation | 2008 - 2020 |
| |
Increase | 798 |
| |
Reconstruction | 1633 |
Addini |
Kita-Hossō sect (en) East Asian Yogācāra (en) |
Suna | Thousand-Armed Thousand-Eyed Avalokiteśvara (en) |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | kakezukuri (en) |
Yawan fili | 12.3 ha |
Muhimman Guraren Tarihi na Duniya | |
Criterion | (ii) (en) da (iv) (en) |
Reference | 688-004 |
Region[upper-roman 1] | Asia and Oceania |
Registration | ) |
Offical website | |
|
Tarihi
gyara sasheAn kafa wurin bauta na Kinyomizu a zamanin Heian.[2] Ya zuwa shekarar 778, wurin ya kasance mallakin Budha Kita-Hosso a karkashin Enchin Shonin. Ya kasance firisti daga Nara (babban birnin Japan daga 710 zuwa 784), wanda akai wa wahayi cewa ya gina wurin bautar a gabar kogin Otowa.[3]
Acikin shekarar 798, Shogun Sakanoue no Tamuramaro ya kara bunkasa wurin bautar ta hanyar sanya wani katafaren dakin taro wanda aka shirya daga fadar Sarki Kammu (r. 781–806). Sarkin ya bar garin Naru a dalilin tsananin ikon da malaman addinin Budha ke da shi akan gwamnatin garin. A wancan lokacin, akwai adawa mai tsanani a tsakanin wurin bautar Budhanci na Kofuku-ji da kuma wurin bauta na Kiyomizu, wanda dukkansu suna da tsananin karfin iko a yankin.[3]
Ginin wurin bautar na yanzu an yi shine a shekarar 1633, wanda Tokugawa Iemitsu ya bayar da umurnin yin ginin.[4] Ba ayi amfani da ƙusa ko daya ba a wajen yin ginin. Ta samo sunanta ne daga wani kogi mai kwarara zuwa sashin tuddai na yankin -wato waterfall a yankin. Kiyomizu na nufin ruwa mai haske ko ruwa mai kyau ko tsafta.[5][6]
Tun asalin wurin bautar tana da alaka da Hossō daga lokacin Nara.[7] Amma an raba wannan alakar a shekarar 1965, masu daukan nauyin wurin bautar na yanzu suna kiran kansu da suna mambobin sashin "Kitahossō".[8]
A yanzu
gyara sasheWurin bautan yana dauke da sauran dakunan bauta da dama, daga cikinsu akwai dakin bauta na Jishu, wanda aka sadaukar don Ōkuninushi, ubangijin soyayya da kuma "kyawawan hadi" - na soyayya.[9] Acikin dakin bauta na Jishu akwai "duwatsun soyayya" guda biyu wanda aka ajiye da nisan mita 10 (30 feet) a tsakaninsu, wanda baki masu fama da kadaici zasu zagaya idonsu rufe. Cin nasara shine isa zuwa wajen dayen dutsen da idanu rufe, wannan na nufin cewa masu ziyara zasu cin ma samun soyayya ko kuma soyayya ta gaskiya.[10] Za'a iya taimkawa mutum wajen yin tafiyar, har ila yau, abokin soyayyar mutum zai iya raka shi.
Ana gudanar da tsubbace-tsubbace da hayaki da kuma rufa ido - omikuji (fadan abunda zai faru a gaba ta takarda) a wajen bautan. Wannan wurin bauta yafi shahara a lokacin bukukuwa (musamman zagayowar Sabuwar Shekara da kuma bikin obon wanda akeyi a lokacin rani), a lokacin da ake samun sabbin baki kuma ana sayar masu da kayan gargajiya.[11]
A cikin shekara ta 2007, Kiyomizu-dera ya shiga cikin zabi 21 don zama daya daga cikin sabbin wuraren al'ajabi guda bakwai na duniya,[12] amma ba'a zabe shi ba a matsayin daya daga cikin wuraren tarihi guda bakwai da suka lashe gasar. An lullube ginin da wani abu mai shara-shara a yayinda ake gyara ta don Wasannin Olympics ta 2020.
Tsarin gini
gyara sasheWurin bautan na nan a yankin tuddan Mount Otowa, a sashin dutsen Higashiyama mountain wanda ya mamayen yankin gabashin Kyoto. Babban dakin yana dauke da katafaren baranda, da dogayen ginshikai, wanda ya fito ta saman tuddai kuma ya bada sura mai kyawun gani. An gina manyan barandu da manyan dakunan taro a zamanin Edo, don tarbar masu zuwa buta da dama.[13]
A karkashin babban dakin bautan akwai Otowa waterfall, inda hanyoyin ruwa guda uku ke shiga cikin wata korama. Baki kan tarbi ruwan su sha wanda ake tsammani yana ikon sanya buruka su zamo gaskiya. Akwai kuma Tainai Meguri, wani dogon kogo mai duhu wanda akace yana wakiltar tumbin bodhisattva Mahāpratisarā.[14][15]
Hotuna
gyara sashe-
Kiyomizu-dera a lokacin kaka
-
Kiyomizu-dera a lokacin sanyi
-
Statuettes of Ksitigarbha (or Jizō) en masse
-
Otowa-no-taki, waterfall da bako ke sha don neman lafiya, tsawon rayuwa, da nasarorin karatu
-
Kiyomizu-dera, Illuminated
-
Dougong kayan gini, Kiyomizu-dera
-
sassaken Dragon a Kiyomizu-dera
-
dama zuwa hagu: Kaisan-do (dakin wanda suka kirkira), Kyo-do (Dakin taro na Sutra) da kuma Sanju-no-to (Bene mai hawa uku na Pagoda)
-
sashin Kyoto da Niōmon daga Kiyomizu-dera
Kara bincike
gyara sashe- Historic Monuments of Ancient Kyoto (Kyoto, Uji and Otsu Cities)
- List of Buddhist temples in Kyoto
- List of National Treasures of Japan (temples)
- The Glossary of Japanese Buddhism for an explanation of terms concerning Japanese Buddhism, Japanese Buddhist art, and Japanese Buddhist temple architecture
- Tourism in Japan
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Historic Monuments of Ancient Kyoto (Kyoto, Uji and Otsu Cities)". Retrieved 2008-12-20.
- ↑ Ponsonby-Fane (1956), p. 111.
- ↑ 3.0 3.1 "Kiyomizu-dera". World History Encyclopedia (in Turanci). Retrieved 2022-07-11.
- ↑ Graham, Patricia J. (2007). Faith and Power in Japanese Buddhist Art. Honolulu: University of Hawaii Press. ISBN 978-0-8248-3126-4. p. 37
- ↑ "Kiyomizu Temple". 2007-04-07. Archived from the original on 2009-04-03. Retrieved 2008-12-18.
- ↑ "Kiyomizudera, Kyoto". Archived from the original on 2009-09-12. Retrieved 2008-12-18.
- ↑ Graham, Patricia J. (2007). Faith and Power in Japanese Buddhist Art. Honolulu: University of Hawaii Press. ISBN 978-0-8248-3126-4. p. 32
- ↑ "Kiyomizu-deploy". Archived from the original on 2017-11-15. Retrieved 2023-06-16.
- ↑ "Kiyomizu Temple". 2007-04-07. Archived from the original on 2009-04-03. Retrieved 2008-12-18.
- ↑ "japanvisitor.com". Retrieved 2010-08-21.
- ↑ "Kiyomizu-dera Temple". Archived from the original on December 10, 2008. Retrieved 2008-12-20.
- ↑ "The Finalists for The Official New 7 Wonders of the World". Archived from the original on 2009-06-01. Retrieved 2009-06-01.
- ↑ Graham, Patricia J. (2007). Faith and Power in Japanese Buddhist Art. Honolulu: University of Hawaii Press. ISBN 978-0-8248-3126-4. p. 80
- ↑ Mukri, Farha (3 April 2019). "From darkness to light at Japan's Kiyomizu-dera". The Hindu. Retrieved 2023-02-12.
- ↑ "Kiyomizu-dera temple is one of Kyoto's must-see attractions!". 13 June 2016.