Kisan kiyashin Chadi da Najeriya, Maris 2020
A ranar 23 ga Maris din shekarar 2020, yan ta'adda masu kishin Islama sun kashe sojoji a Chadi da Najeriya.
| ||||
Iri |
bomb attack (en) shooting (en) | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 23 ga Maris, 2020 | |||
Wuri |
Cadi Jihar Borno | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 168 |
Harin a sansanin Bohama
gyara sasheTun da karfe 5 na safe ne 'yan Boko Haram suka kai hari a sansanin sojojin Bohama da ke wani tsibiri a tafkin Chadi.[1] An kai harin ne daga bangarori huɗu, inda suka kai hari da sojoji kusan 400. Mayakan jihadin sun mamaye sansanin ne bayan shafe sa'o'i bakwai ana gwabza faɗa. An aike da sojoji daga garin Kaïga Kindjiria domin farfado da sansanin da aka yi wa kaca-kaca amman sun faɗa tafkin Mayaƙan inda aka yi musu kwanton ɓauna. A jimilce sojojin Chadi 98 ne suka mutu, 47 suka jikkata, sannan an lalata motoci 24.[2][3][4][5]
Kwanton ɓauna a Gorgi
gyara sasheDa yammacin ranar ne wasu ‘yan tada kayar baya ɗauke da manyan bindigogi suka yi wa wata motar ɗaukar kaya kwanton ɓauna tare da kona ta inda suka kashe sojojin Najeriya kusan 70 a ƙauyen Gorgi da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.[6] An jikkata wasu sojoji da dama tare da yin garkuwa da wasu.[6] Motar dai na cikin ayarin motocin da ta taso daga Maiduguri zuwa sansanin mayakan ISIL. [6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Boko Haram kills almost 100 soldiers in seven-hour attack in Chad
- ↑ "Derrière l'attaque jihadiste au Tchad". 6 April 2020.
- ↑ "Tchad - Boko Haram : l'Armée revoit le bilan à la hausse, 98 soldats tués".
- ↑ "Au Tchad et au Nigeria, le double carnage de Boko Haram".
- ↑ "Lac Tchad : Près de 100 militaires tués dans une attaque de Boko Haram". 25 March 2020.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 Militant ambush kills at least 70 soldiers