Khelil Bouhageb (27 ga Agustan shekarar 1863 a Tunis - 8 ga Fabrairu shekarata 1942 a La Marsa ) ɗan siyasan Tunisiya ne kuma mai kawo canji. Ya yi mulki a matsayin Firayim Ministan Tunisia daga 1926 zuwa shekarar 1932, bayan mutuwar Mustapha Dinguizli. Bouhageb ɗa ne ga Sheikh Salem Bouhageb ; dan uwansa likita ne mai sunaHassine Bouhageb.

Khelil Bouhageb
Grand Vizier of Tunis (en) Fassara

1926 - 1932
Mustapha Dinguizli - Hédi Lakhoua
Mayor of Tunis (en) Fassara

1926
Mustapha Dinguizli - Chedly El Okby (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Tunis, 27 ga Augusta, 1863
ƙasa Beylik of Tunis (en) Fassara
French protectorate of Tunisia (en) Fassara
Mutuwa La Marsa (en) Fassara, 8 ga Faburairu, 1942
Ƴan uwa
Mahaifi Salem Bouhageb
Abokiyar zama Princess Nazli Fazl (en) Fassara
Ahali Hassine Bouhageb (en) Fassara
Karatu
Makaranta Sadiki College (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Khalil Bouhageb

Tarihin rayuwa

gyara sashe

Yayi karatu a makarantar Sakandare ta Sadiki da ke Tunis sannan kuma ya yi karatu a makarantar sakandaren Saint-Louis da ke Paris. Ya zama memba na Hukumar Daraktocin Khaldounia a cikin shekarar 1898, yayi aure a ranar 5 ga watan Afrilun shekarar 1900 a Alkahira, ya auri Gimbiya Nazli Fazıl, wacce ta kasan ce jika ce ga sarki Mehemet Ali.

A ranar 22 ga Afrilu 1915 ya zama shugaban kotun Tunis sannan kuma shugaban karamar hukumar Tunis (Sheikh El Medina) a ranar 19 ga watan Oktoba na wannan shekarar. An nada shi a matsayin Ministan Alkalami a ranar 22 ga Mayu 1922 da Grand Vizier na Tunis a ranar 3 ga Nuwamba 1926 bayan mutuwar Mustapha Dinguizli. Ahmed II Bey ya kore shi a cikin 1932 saboda 'yancin kansa, wanda aka azabtar da makircin mukarraban Bey.

Khelil Bouhageb bai bar zuriya ba. An binne shi tare da mahaifinsa, Sheikh Salem Bouhageb, da dan uwansa, Dr. Hassine Bouhageb.

Manazarta

gyara sashe