Khalda Saber
Khalda Saber wata malamar Sudan ce kuma mai fafutukar kare hakkin bil Adama wacce ta yi aiki tare da wata kungiya mai zaman kanta kan harkokin kare hakkin mata. Ta kasance daya daga cikin matan da suka jagoranci zanga-zangar adawa da mulkin shugaba Omar al-Bashir na tsawon shekaru 30 wanda ya kai ga kwace gwamnati da sojoji suka yi.[1] Saber ta karfafa gwiwar malamai da mata da ta hadu da su a kan tituna a birnin Port Sudan a lokacin da take tafiya makarantar da ta koyar da su shiga cikin masu fafutukar tabbatar da dimokradiyya.[2] “Ina gaya musu cewa babu abin da za mu yi asara, idan aka kwatanta da abin da muka riga muka yi asara. Ina gaya musu cewa dole ne mu fito kan tituna, mu yi zanga-zanga kuma mu nuna kin amincewa da abin da ke faruwa."[3] [4]
Khalda Saber | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | female teacher (en) , Mai kare ƴancin ɗan'adam da gwagwarmaya |
Kamawa (Arrest)
gyara sasheWatanni biyu da gudanar da zanga-zangar ta Saber, jami'an tsaro na farin kaya suka tare su a cikin wata motar safa, sannan aka kai su babban ofishin hukumar tsaro da leken asiri na karamar hukumar.[5] Ta shafe kwanaki 40 tana tsare tare da wasu mata dubu da suka jagoranci zanga-zangar adawa da al-Bashir a wani sabon reshe da aka gina a gidan yari a babban birnin kasar, Khartoum.[6]
Ƙaura
gyara sasheBayan sakinta daga tsare ta, ta shiga wani zaman dirshan a wajen hedikwatar sojoji dake birnin Khartoum a wata zanga-zangar. Ta samu barazana ga rayuwa da iyalai daga Rapid Support Forces (RSF) wata kungiyar sa-kai da ta balle daga mayakan Janjaweed da al-Bashir ya yi amfani da shi a rikicin yankin Darfur na Sudan. [7][8] Saber ta tsere daga kasar tare da mijinta da 'ya'yanta mata biyu zuwa birnin Alkahira na kasar Masar a zaman gudun hijira kwanaki biyu bayan da sojoji suka hambarar da al-Bashir. Saber ta tattara bayanan take haƙƙin ɗan Adam na RSF, musamman akan mata, ta hanyar sheda kafin da lokacin boren. [9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "In new Sudan, Women Want More Freedom, Bigger Political Role | Voice of America - English" . www.voanews.com . Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "In new Sudan, Women Want More Freedom, Bigger Political Role | Voice of America - English" . www.voanews.com . Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "In new Sudan, women want more freedom, bigger political role" . The Washington Times . Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "The Women's Revolution: Female Activism in Sudan" . Harvard International Review . 2020-05-25. Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "Khalida Saber Detained Incommunicado in Ongoing Crackdown on Sudanese HRDs" . Front Line Defenders . 2019-02-14. Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "Khalida Saber Detained Incommunicado in Ongoing Crackdown on Sudanese HRDs" . Front Line Defenders . 2019-02-14. Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "In new Sudan, women want more freedom, bigger political role" . Egypt Independent . 2019-09-19. Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "Khalda Saber" . KSLNewsRadio . Retrieved 2021-02-02.
- ↑ "Sudan Strives to Stop Violence Against Women | Voice of America - English" . www.voanews.com . Retrieved 2021-02-02.