Keita! l'Héritage du griot (fim)
Keïta! l'Héritage du griot Keïta! l'Héritage du griot (Sunan da Hausa: Keita! Muryar Griot) fim ne na shekarar 1995 naBurkina faso wanda Dani Kouyaté ya ba da Umarni, jaruman shirin sun haɗa da Sotigui Kouyaté. Fim ɗin wani cigaba ne na shirin Epic of Sundiata na ƙarni na 13, wanda aka haɗa tare da al'amuran griot yana ba da labari ga ƙaramin yaro. [1]
Keita! l'Héritage du griot (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1995 |
Asalin suna | Keïta ! L'Héritage du griot |
Asalin harshe | Faransanci |
Ƙasar asali | Faransa |
Characteristics | |
Genre (en) | fantasy film (en) |
Launi | color (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Dani Kouyaté (en) |
Marubin wasannin kwaykwayo | Dani Kouyaté (en) |
'yan wasa | |
Samar | |
Mai tsarawa | Sahelis Productions (en) |
Other works | |
Mai rubuta kiɗa | Sotigui Kouyaté (en) |
Kintato | |
Narrative location (en) | Afirka |
External links | |
Makirci
gyara sasheKeita Mabo Keïta (Dicko) ya bi Mabo Keïta (Dicko), wani yaro ɗan shekara 13 da ke zama a gidan bourgeois a birnin Ouagadougou kuma yana makaranta mai kyau. Ya haɗu da Djeliba Kouyate wani griot wanda yake so ya gaya wa matashi Keita asalin sunansa da ke da alaƙa da Sundjata Keita. Kouyate ya fara bayar da tarihinsa ne da tatsuniyar halittar Mandeng Yayin da dukkan halittu suke taruwa a sabuwar duniya da aka kafa mutum ya bayyana wa talakawa cewa yana son ya zama sarkinsu. Tsohon griot ya ba da labarin yadda dangin Keita suka fito daga buffalo, har yanzu tsuntsaye suna kallonsa, da kuma yadda mutane ke da tushen da ke kwance a ƙasan duniya. [2]
Yan wasan kwaikwayo
gyara sashe- Seydou Boro as Sundjata Keita
- Hamed Dicko a matsayin Mabo Keïta
- Abdoulaye Komboudri a matsayin Drissa Fafana
- Sotigui Kouyaté a matsayin Djeliba Kouyate; Sotigui Kouyaté shine mahaifin daraktan fim din, Dani Kouyaté
- Claire Sanon a matsayin Sitan
- Blandine Yaméogo a matsayin Sogolon
Shiryawa
gyara sasheDani Kouyaté ya bada umurnin wasu gajerun fina-finai kafin a saki Keïta, fasalinsa na farko mai tsayi. [1] Taken aikin fim ɗin shine Keita: Daga Baki zuwa Kunne . [3] An ɗauki shirin fim din a garuruwan Ouagadougou, Sindou, da kuma Ouahabou . [1] Mataimakin darakta Alidou Badini.[1] The assistant director was Alidou Badini.[4]
Kyautuka da Tsokaci
gyara sasheKeita! Ya sami Kyautar Fina Finai Na Farko daga Panafrican Film and Television Festival na Ouagadougou (Fespaco) kuma an ba shi lambar yabo ta Junior a bikin Fim na Cannes . [1] Jaridar New York Times ta yabawa fim din, tana mai cewa "ya yi nasara sosai wajen raya... tarihi." A cikin wata hira ta 1995, Kouyate yayi tunani a kan gogewa da sharhi kan al'ummar gargajiya, yana mai cewa:
Sometimes when you don't know where you're heading, you have to return to where you came from in order to think things over before continuing your journey. Today, with all the things happening to her, Africa has trouble finding which direction to take—modernity, tradition, or some other road. We are not really capable of digesting all these things. We don't know who we are, and we don't know where we are going. We are between two things. Between our traditions and our modernity.[5]
Bayanan kula
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Gugler 2003
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-17. Retrieved 2024-02-16.
- ↑ Gugler 2003
- ↑ "Alidou BADINI". Africutlures. Retrieved 2012-03-12.
- ↑ Baaz & Palmberg 2001, p. 99