Kayode Adebowale
Kayode Oyebode Adebowale FRSC (an haife shi ranar 11 ga watan Janairu, 1962). Farfesa ne kuma masanin kimiya na Najeriya kuma shine mataimakin shugaban jami'ar Ibadan na 13.[1] A cikin Oktoba 2021 ya zama Mataimakin Shugaban Jami'ar Ibadan,[2]wanda ya taɓa zama mataimakin shugaban jami'ar Ibadan, kuma a matsayin shugaban tsangayar kimiyya a wannan cibiyar.[3]
Kayode Adebowale | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 11 ga Janairu, 1962 (62 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | scientist (en) da academic administrator (en) |
Employers | Jami'ar Ibadan |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | Makarantar Kimiyya ta Najeriya |
Yaranta da Ilimi
gyara sasheAn haifi Farfesa Kayode Adebowale a ranar 11 ga Janairun 1962 kuma shi dan asalin jihar Gateway ne, Ogun a Yammacin Najeriya. Ya yi karatun firamare a St. Marks Primary School, Oke-Ijaga, Ijebu Igbo tsakanin 1967 zuwa 1972 yayin da ya yi sakandire a Makarantar Grammar Ayedaade, Ikire tsakanin 1973 zuwa 1978. Ya yi digirinsa na B.Sc a Chemistry a 1984 a Jami'ar Ibadan yana da shekaru 22. Ya samu digirinsa na biyu da kuma Ph.D daga jami'a guda a 1986 da 1991. Ya fara karatunsa a matsayin Mataimakin Digiri a Jami’ar Ibadan sannan ya zama Farfesa a fannin sinadarai na masana’antu a shekarar 2006.
Rayuwar Ilimi
gyara sasheYa taba zama malami a Jami'ar Fasaha ta Tarayya. Ya taba zama Mataimakin Shugaban Jami’ar Ibadan (Administration). Farfesa Adebowale, MNI, FRSC, FAS, FAvH, FCSN, FSAN, FPIN shine shugaban jami'ar Ibadan na 13.
A ranar Alhamis, 14 ga Oktoba, 2021, Shugaban Majalisar kuma Shugaban Jami’ar, Cif Dr. John Odigie-Oyegun, ya sanar da nadin Farfesa Kayode Adebowale a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar na 13.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Osinusi, Femi (2021-10-14). "(BREAKING): Professor Adebowale emerges new Vice Chancellor of University of Ibadan". Tribune Online. Retrieved 2022-09-24.
- ↑ "Kayode Adebowale emerges new UI Vice Chancellor". Punch Newspapers. 2021-10-14. Retrieved 2022-09-24.
- ↑ ""Past and Present Deans of Faculties | UNIVERSITY OF IBADAN". www.ui.edu.ng. Retrieved 2022-09-24". Archived from the original on 2022-09-24. Retrieved 2022-09-24.