Kavidi Wivine N'Landu
Kavidi Wivine N'Landu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 20 century |
ƙasa | Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, maiwaƙe da marubuci |
Kavidi Wivine N'Landu mawakiya shayari ce kuma 'yar siyasa daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. A shekara ta 1980 an nada ta Babbar Sakatariya na Ma'aikatar Harkokin Mata a lokacin mulkin Mobutu Sese Seko. A yayin daukakar Laurent Kabila, ta gudu zuwa Afirka ta Kudu. A matsayinta na mawakiya, ta yi fice da jerin wakokinta mai suna Leurres et Lueurs.
A watan Afrilun shekara ta 2006, ta kasance daya daga cikin 'yan takarar da fito takara a zaben shugaban kasan Kongo na shekara ta 2006.